Hajji 2026: NAHCON Ta Kammala Samar Da Masaukin Alhazan Nijeriya Kafin Cikar Wa’adin Saudiyya
[ad_1]
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da kammala dukkan shirye-shiryen samar da masaukin miniyyata Hajjin 2026 a Makkah da Madinah, tun kafin cikar wa’adin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana hakan ga masu ruwa da tsaki da alhazai da kuma manema labarai a yau Litinin 2, ga Febarairun 2026, inda ya jaddada cewa kammala tanadin masaukin ya nuna irin jajircewar Hukumar wajen bin ƙa’idoji da tsare-tsaren Saudiyya.
- Wang Yi Ya Tattauna Da Sakataren Hukumar Tsaro Ta Rasha
- Tsaro: An Sake Buɗe Kwalejin Jihar Kwara Bayan Rufeta A Baya
Mai taimaka wa Shugaban NAHCON kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Mu’azu, ya ce kammala ɗora bayanan masauki da kuma amincewa da su daga Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ya biyo bayan umarnin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda ya umurci a hanzarta kammala muhimman shirye-shiryen Hajji a kan lokaci domin kare muradun Nijeriya.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yaba da jagoranci da goyon bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa tare da nuna godiya kan rawar da tawagar manyan jami’ai da aka tura Saudiyya da Hukumar Gudanarwar NAHCON da tawagar Nusuk Masar da kuma shugabannin Ƙungiyar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihohi da ma’aikatan NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki suka taka wajen kammala tanadin wannan masaukin.
Da kammala wannan muhimmin shiri, Nijeriya ta samu nasarar kulle masaukin alhazanta na Hajjin 2026, lamarin da ya sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da suka cika wannan sharadi a kan lokaci kamar yadda dokokin Saudiyya suka tanada.
Hukumar ta bayyana cewa yanzu haka ta fara mataki na gaba na shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, domin tabbatar da tafiyar da ibadar Hajji cikin tsari da sauƙi kuma cikin nasara ga alhazan Nijeriya.
[ad_2]
Source link