Kotu ta yi wa mutum 3 daurin shekara 6 kan lalata da ƙananan yara a Kano
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, ta yanke wa wasu maza uku hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samun su da laifin lalata ƙananan yara.
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ce, ta gurfanar da mutanen, wanda hakan ya kai ga yanke musu hukunci.
Alkalin kotun, Mai shari’a S.M. Shuaibu, ya yanke wa kowanne daga cikinsu hukuncin daurin shekaru shida ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka yankewa hukunci, Jibrin Adamu mai shekaru 67 daga unguwar Hotoro Danmarke a Kano, an same shi da laifin ɗaukar wata yarinya mai shekaru 11 daga Walawai Hotoro a Ƙaramar Hukumar Nassarawa a watan Agustan 2025 tare da lalata da ita.
An same shi da laifi ne ƙarƙashin Sashe na 16(1) na Dokar Hana Safarar Mutane ta shekarar 2015.
Sauran biyun, Kanta Muhammadu mai shekaru 65 da Ishaya Hassan mai shekaru 40, su ma an same su da laifin ɗaukar mutane domin lalata da su ƙarƙashin dokar.
An gurfanar da su tare kuma aka yanke wa kowannensu hukunci a rana daya a shari’o’i daban-daban.
Hukumar NAPTIP ta shiyyar Kano, ta ce wannan hukunci wata babbar nasara ce a yaƙin da ake yi da safarar mutane da cin zarafin al’umma a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link