Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri
Tsohon Kwaminsihan Sufuri na jihar Legas Dakta Frederic Oladeinde, ya ce, kaddamarwa da kuma wanzar da tsarin fasahar Electronic Call-up da Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa NPA ta yi, hakan ya samar da sauki, wajen shige da fice, manyan motoci, cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talatar da ta gabata, Frederic ya yi nuni da cewa, samar da fasahar, ta kawo karkahen jinkirin safarar kaya da cunkoso da sauwake wahalarhalun, da aka shafe shekaru, ana fuskaanta.
- Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
- Yadda Tayar Jirgin Sama Ta Ɓalle Bayan Tashinsa A Amurka
A cewarsa, hakan ya kuma samar da sararin wajen ajiye manyan motoci, a cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.
Oladeinde yaci gaba da cewa, kafin a samar da fasahar, dirbobin manyan motoci da ke shiga cikin Tashin, na kawai ajiye motocinsu ne, barkatai wanda hakan ke haifar da dogayen layuka da kuma haifar da tsaiko, wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Ya ci gaba da cewa, bayan wanzar da fasahar a cikin ‘yan watanni, hatta gwamnatin jihar, ta samu kaso 90, na yin biyyar yin rijista, a tsakanin direbobin manyan motocin.
Oladeinde ya bayyana cewa, nasarar wannan fasahar, ta dogara ne kan hadain kai da hukumomin gwamnatin jihar da kamfanoni masu zaman kansu da masana’antu da kuma masu ruwa da tsaki, suka bayar.
Koda yake dai, Oladeinde, ya sanar da cewa, wasu sun nuna tirjiya wajen wanzar da fasahar, inda wasu direbobin manyan motocin, sukai ta yunkurin gayawa ta bayan fage, domin kin sayen tikitin, shiga cikin Tashoshin.
Ya yi nuni da cewa,a duk lokacin da aka samar da wani abu sabo, yak an fuskanci turjiya, amma abinda ya fi da cewa, shi ne, a ci gaba da wanzar da shi, yadda ya kamata, domin a samu cin nasarar, da aka sanya a gaba.
Ya sanar da cewa, gwamnatin jihar na ci gaba da daukar matakai, domin ganin ana yin biyayya da wannan sabuwar fasahar, musammman domin samar da kan hanyoyi a jihar.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki, da su sanya kishi, wajen yin biyayya da wannan sabuwar fasahar.
“Ya kamata gwamnati, ta dauki wannan tsarin, a matsayin na dogon zango, kuma dole ne, a goya tsarin baya, domin a cimma burin da aka sanya a gaba, ma’ana dai, samar da kyakyawan yanyi, a hanyoyi da kuma bin ka’ida, a tsakanin masu ruwa da tsaki.