NPFL: Barau FC ta tashi babu ci tsakaninta da Bendel Insurance
[ad_1]
Ƙungiyar kwallon kafa ta Barau FC ta ci gaba da zama a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) bayan ta tashi babu ci a wasanta da Bendel Insurance a wasan mako na 23 da aka buga a filin wasa na Samuel Ogbemudia, da ke Benin City, jihar Edo.
An buga wasan a ranar Alhamis, inda kungiyar ta taka rawar gani a gidan masu masu masaukin baki, suka kuma samu maki mai muhimmanci.
Sakamakon ya nuna cewa kungiyar ta yi wasanni hudu a jere ba tare da an ci su ko da a wasa daya ba ba a zagaye na biyu na kakar firimiyar ta 2025/2026.
Ko a baya ma, Barau FC ta doke Niger Tornadoes, sannan ta yi kunnen doki sau uku a jere da Enyimba a Aba, Bayelsa United a Kano, sannan yanzu da Bendel Insurance a Benin.
Da yake magana bayan wasan, kocin kungiyar, Eugene Agagbe, ya yaba wa ’yan wasansa bisa jajircewarsu a wasannin.
“Ina yaba wa ’yan wasana. Ba sabu ne mai sauƙi ba a samu maki a waje, amma tabbas ’yan wasan sun bi dabarun da na tsara, shi ya sa muka samu wannan sakamakon,” in ji shi.
Agagbe ya ce yanzu hankalin ƙungiyar ya koma kan wasa na gaba da za su buga da Ikorodu City a Kano, wanda aka shirya yin shi mako mai zuwa a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano.
Da wannan canjaras din na Alhamis, Barau FC ta hau matsayi na 15 a teburin NPFL da maki 27 a wasanni 23, yayin da suke ci gaba da fafutukar guje wa ficewa daga gasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link