Kano Pillars ta doke Katsina United a gasar Firimiyyar Najeriya

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Katsina United 1-0 ranar Laraba a wasan mako na 23 a gasar Firimiya ta Najeriya.

Ahmed Musa ne ya ci ƙwallon daf da tashi a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata a Jihar Kano.

A haɗuwar ƙarshe da ƙungiyoyin biyu suka yi a cikin watan Satumban bara, Katsina United ce ta ci Kano Pillars 1-0 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Da wannan sakamakon ƙungiyar Pillars da ake laƙabi da ‘Sai Masu Gida’ ta koma mataki na 18 a teburin Firimiyar ta Najeriya da maki 25.

Ita kuwa Katsina United mai maki 30 tana mataki na 11, amma tana da kwantan wasan a hannu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *