Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
[ad_1]
Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna damuwarta ga mutanen garin Kurmin Wali da ke Jihar Kaduna, bayan satar mutane Sama da 100, inda lamarin ya jefa wasu mazauna cikin tashin hankali.
Tawagar Majalisar sun kai ziyara ne karkashin jagorancin Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Lawal Adamu Usman, wanda ya wakilci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a wani ziyara ta nuna ta’aziyya da kuma duba halin da al’umma ke ciki.
- Muhimmanci Da Amfanin Shan Rake Ga Lafiyar Dan Adam
- Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi
A yayin ziyarar, Sanata Lawal Adamu Usman ya isar da sakon damuwar Shugaban Majalisar kan wannan lamari, inda ya tabbatar wa mutane da shugabannin al’umma cewa Majalisar Dattawa na Nijeriya zata tallafawa al’ummar da abin ya shafa da kuma tabbatar da tsaron su. Haka kuma, ya yi alkawarin kawo kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.
A cikin ziyarar, Sanatan ya fara ne da kai ziyara zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko, Kaduna, inda ya gana da wadanda suka ji rauni. Ya yi ta’aziyya ga wadanda suka samu rauni da iyalansu, tare da basu kalaman kwarin gwiwa da addu’o’i don samun saukin murmurewa.
Bayan ziyarar asibiti, Sanata Lawal Adamu Usman ya nufi Fadar Agum Adara, inda ya gana da shugabannin al’umma, ciki har da Agum Adara da Mai Unguwar Kurmin Idom. Sanatan ya yi ta’aziyya ga shugabannin gargajiya da mazauna garin kan wannan mummunan lamari, inda ya bayyana abin a matsayin abin takaici da damuwa sosai.
Ya kuma tabbatar da cewa Majalisar Dattawa, karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro domin karfafa tsaro a yankin da kuma hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
A yayin ziyarar, Agum Adara ya gode wa Majalisar Dattawa da Sanata Lawal Adamu Usman saboda nuna damuwa da al’ummar a wannan mawuyacin lokaci.
Ya bayyana cewa ziyarar ta kasance wata shaidar hadin kai, inda kasancewar wakilan Majalisar ta ba al’umma sabon kwarin gwiwa da tabbacin samun goyon baya.
Mazauna Kurmin Wali sunyi marabi da tawagar Majalisar Dattawa tare da rokon ci gaba da tallafin gwamnati, ciki har da karin jami’an tsaro da kuma kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.
[ad_2]
Source link