Atiku Ya Gana Da Shugabannin ADC, Ya Yi Alƙawarin Samar Wa Nijeriya Kyakkyawar Makoma


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin jam’iyyar All Democratic Congress (ADC) daga Jihar Kebbi a ranar Laraba.

Ya wallafa wannan bayani a shafinsa na X, inda ya gode musu bisa ziyarar da suka kai masa.

  • Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Sake Jaddada Tabbatar Da Daidaitacciyar Kasuwa
  • Gwamna Lawal Ya Fara Ganawa Da Manyan Jiga-jigan PDP A Zamfara

Ya ce ya yi matuƙar farin ciki da yadda tattaunawar ta gudana.

Atiku ya bayyana cewa sun tattauna kan hanyoyin ƙarfafa jam’iyyar ADC da kuma yadda za su doke jam’iyyar APC mai mulki a zaɓe mai zuwa.

Ya kuma ce burinsu shi ne samar da kyakkyawan shugabanci da nagartaccen mulki ga ’yan Nijeriya.

A cewarsa, jam’iyyar ADC na ƙoƙarin zama jam’iyya ta gari ga ’yan ƙasa tare da inganta rayuwar al’umma.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *