Zhao Leji Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Senegal
Babban dan majalisar gudanarwar kasar Sin Zhao Leji, ya zanta da shugaban majalisar dokokin kasar Senegal Malick Ndiaye, jiya Talata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Zhao, wanda kuma shi ne shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Senegal wajen aiwatar da muhimman kudurori da aka cimma tsakanin jagororin kasashen biyu, da sakamakon taron dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na birnin Beijing, da kara saita cikakken tsarin hadin gwiwa bisa matsayin koli a fannin cudanyar Sin da Senegal, tare da haifar da karin gudummawar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani daga dukkanin fannoni.
A nasa bangare kuwa, mista Ndiaye cewa ya yi, Senegal na nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, tana matukar martaba muhimman shawarwarin nan guda hudu na raya duniya da kasar Sin ta gabatar, kuma a shirye take ta ci gaba da ingiza gina shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar, da karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)