Gwamna Abba zai yi nadamar barinmu — Kwankwaso
[ad_1]
Jagoran jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da muƙarrabansa za su yi nadamar barin jam’iyyar a nan gaba.
Kwankwaso ya ce ficewar gwamnan daga NNPP ta bai wa mutane da dama mamaki.
“Mutane da dama sun ɗauka wata yarjejeniya ce aka ƙulla tsakanina da shi, ko tsakaninsa da wasu. A wasu lokuta na kan kasa yarda da yadda abubuwa ke tafiya,” in ji Kwankwaso.
Gwamna Abba ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026, bayan ya sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar 23 ga watan Janairu.
Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan duba halin da siyasar Najeriya ke ciki da kuma abin da yake ganin zai kawo ci gaba ga al’ummar Jihar Kano.
Sai dai a hirarsa da BBC Hausa tun bayan ficewar gwamnan, Kwankwaso ya bayyana matuƙar bacin ransa kan lamarin.
“Ya miƙa amincewar ’yan jam’iyyar NNPP da al’ummar Kano ga ’yan Gandujiyya ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba,” in ji Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa dukkanin dalilan da gwamnan ya bayar kan barin jam’iyyar abubuwa ne da za a iya warware su ta hanyar tattaunawa.
“Abubuwan da ya kawo, ta hanyar haƙuri da fahimtar juna za a iya magance su,” ya ce.
Kwankwaso ya kuma ƙaryata iƙirarin cewa akwai rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta NNPP.
“A iya sanina, babu jam’iyyar da ta fi NNPP zaman lafiya da kwanciyar hankali. Babu wata jam’iyya da ba ta da rikice-rikece,” in ji shi.
Game da waɗanda suka fice NNPP amma har yanzu suna iƙirarin biyayya ga tsarin Kwankwasiyya, Kwankwaso ya ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.
“A bayyana yake akwai haske da duhu a Kano. Idan kana son yin Kwankwasiyya, ka tsaya inda Kwankwasiyya take,” in ji Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa irin tarbar da Ganduje, ya yi wa Abba bayan komawarsa APC alama ce ta raunin siyasa.
“Da Ganduje yana da ikon ɗaga hannun mutum da ya yi hakan a 2019 da 2023,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso ya jaddada cewa Kano har yanzu na tare da NNPP, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ƙulla ƙawance domin sake gyara makomar ƙasar nan.
“Na tabbata ko da bai dawo ba, zai yi nadamar barinmu.”
Kwankwaso na daga cikin fitattun ’yan siyasa a Arewa, kuma yana da miliyoyin magoya baya, musamman matasa, ta hanyar tafarkin Kwankwasiyya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link