Firaministan Kasar Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
Bisa gayyatar Firaministan kasar Sin Li Qiang, Firaministan kasar Birtaniya Keir Starmer zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 28 zuwa 31 ga Janairun nan, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Talata.
Mai magana da yawun ma’aikatar Guo Jiakun ya bayyana a taron manema labarai na yau da kullum cewa, kiyaye sadarwa da karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Birtaniya, wadanda dukkansu membobi ne na dindindin a Kwamitin Sulhun MDD, na cika muradun al’ummomin kasashen biyu tare da ba da gudummawa ga zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ci gaba a duniya.
A lokacin ziyarar Starmer, wacce ita ce ta farko da wani firaministan Birtaniya zai kawo Sin cikin shekaru takwas, Shugaba Xi zai gana da shi, kana Firaminista Li zai tattauna da shi, sannan shugaban majalisar dokokin kasar Sin Zhao Leji shi ma zai gana da shi, kamar yadda Guo ya bayyana, yana mai cewa bangarorin biyu za su yi tattaunawa mai zurfi kan dangantakar kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi muradunsu na bai-daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)