Shugaba Xi Ya Bayyana Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Tsarin Cudanyar Sassa Kasa Da Kasa Bisa Jagorancin MDD


Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar kasarsa, ta yin aiki tare da kasar Finland, wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa kasa da kasa bisa jagorancin MDD, da matukar biyayya ga odar duniya bisa dokar kasa da kasa, ta yadda za a kai ga yin hadin gwiwar tinkarar kalubalolin duniya.

Xi, ya yi tsokacin ne a Talatar nan, yayin ganawarsa da firaministan Finland Petteri Orpo, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin. A cewar shugaban na Sin, kasarsa ta sha alwashin yin aiki tare da Finland, wajen ingiza daidaito, da ra’ayin yawaitar bangarori masu fada-a-ji a duniya, tare da raya tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya mai haifar da gajiya ga kowa, kuma mai hade dukkanin sassa. (Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *