APC Ta Musanta Zargin Yi Wa Bello Turji Rajistar Katin Zama Ɗan Jam’iyyar A Zamfara

[ad_1]

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta musanta zargin yi wa fitaccen Shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji katin shaidar zama ɗan jam’iyyar da aka ce yana ɗauke da suna da hotonsa, yana mai bayyana katin a matsayin jabu, kuma wani mugun shiri da aka shirya don ɓata sunan jam’iyyar.

Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Yusuf Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin, yana mai cewa, katin shaidar zama ɗan jam’iyyar na bogi ne, kuma aikin marasa kishin ƙasa ne da ke neman ɓata aikin rajistar ta yanar gizo da jam’iyyar ke yi.

  • An Tsare Shugaban KANSIEC Da Wasu Biyu A Gidan Yari Bisa Zargin Karkatar Da Kuɗi Naira Biliyan 1
  • Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Gudanar Da Aikin Duba Lafiyar Marayu Kyauta A Zanzibar

A cewarsa, “Wannan aikin miyagun mutane ne marasa kishin ƙasa waɗanda ba su gamsu da yadda ake gudanar da rajistar ‘yan jam’iyyar APC cikin sauƙi, nasara da kuma tsari mai kyau a Jihar Zamfara ba.

“Ga masu lura ta fahimta, za a gane katin bogi ne. Misali, lambar “26”, wacce ake zargin tana nufin kwanan wata, 26 ga Janairu, abin a lura da ita ne sosai. Haka kuma, hoton da aka yi amfani da shi, hoto ne tsoho da ya gama karaɗe shafukan sada zumunta, wanda hukumomin tsaro da ‘yan Nijeriya suka san shi sosai.”

Kakakin APC, ya ƙara bayyana cewa, babu wani mutum da za a iya yi wa rijista a matsayin mamba na jam’iyya ba tare da ingantacciyar Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) ba, wanda Turji ba shi da ita.

“Daga bayananmu na rajistar yau (27 ga watan Janairu) a mazaɓar Unguwar Kware, babu lambar shaida da ta fara da ’26’. Lambobin mambobin APC na Jihar Zamfara sun fara ne da lambar ’36’, ba ’26’ ba,” in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *