Kotu Ta Umarci Ma’aikatan Birnin Tarayya Su Dakatar Da Yajin Aikin Da Suke Yi

[ad_1]

Kotun Ma’aikata ta Ƙasa (NICN) da ke Abuja ta umarci ma’aikatan Babban Birnin Tarayya, ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwar Ƙungiyoyin Ma’aikata (JUAC) da su dakatar da yajin aikin da suke yi nan take.

Hukuncin ya biyo bayan shigar da ƙara da Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi a kan shugabannin JUAC, Rifkatu Iortyer da Abdullahi Umar Saleh, domin hana ƙungiyar shiga yajin aiki da hana gudanar da aiki.

  • ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Tare Da Kashe Ɗan Kasuwa A Kano
  • Da Gaske Ne Wasu Jami’ai 16 Sun Yi Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu — DHQ

Alƙalin kotun, Justice E.D. Subilim, ya ce duk da cewa akwai matsaloli da suka shafi ƙwadago, haƙƙoƙin ma’aikata, ya ce babu buƙatar ci gaba da yajin aikin tun da an shigar da ƙara a kan lamarin.

Ya ce dole a dakatar da yajin aikin idan ya kaasance lamarin na gaban Kotun Ma’aikata ta Ƙasa.

Kotun ta bayar da umarnin dakatar da yajin aikin, tare da tilasta wa ƙungiyar da su dakata har zuwa lokacin yanke hukunci.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa 23 ga watan Maris, 2026.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *