Hafsoshin soji 16 za su fuskanci hukuncin kisa

[ad_1]



Hafsoshin sojin Najeriya aƙalla 16 za su fuskanci hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai bisa laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa binciken da ta kammala bayan tsare waɗanda ake zargin ya same su da laifin yunƙurin kifar da gwamnati.

Wasu tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya da muka zanta da su sun bayyana cewa hukuncin kisa shi ne abin da dokar aikin sojin ƙasar ta tanada kan duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin juyin mulki.

A watan Oktoban bara ne rahoto ya ɓulla cewa Rundunar Sojin Nijeriya, ta hannun Hukumar Binciken Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta tsare wasu hafsoshinta 16 masu muƙamin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar kan zargin yunƙurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.

Aminiya ta ruwaito a ranar Litinin cewa kwamitin da rundunar ta kafa ya kammala bincikensa tare da miƙa rahotonsa ga Shugaba Tinubu domin ɗaukar mataki na gaba.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo-Janar Samaila Uba, ya tabbatar cewa kwamitin ya miƙa rahotonsa ga “mahukuntan da suka dace.”

Kotun soji za ta yanke musu hukunci

Sanarwar da Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar a ranar Litinin ta ce za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soji domin yanke musu hukuncin da dokokin aikin soji suka tanadar.

Ya ce, “Rundunar Sojin Najeriya tana sanar da al’umma cewa an kammala binciken tare da gabatar da rahoton ga mahukunta da suka dace kamar yadda doka ta tanadar.

“An kammala zuzzurfa kuma cikakken bincike kan duk waɗanda ake zargin, bisa tanadin dokokin aikin soji.

“Binciken ya gano cewa daga a cikin waɗanda ake zargi da hannu a yunƙurin hamɓarar da gwamnati, wanda yin hakan ya saɓa wa tsarin aikin sojin Najeriya; don haka za a gurfanar da su a gaban kotun soji da sauran dokokin ƙasa.”

Ya bayyana cewa an sanar da jama’a halin da ake ciki ne domin komai ya kasance a fili da kuma tabbatar da adalci, a yayin da rundunar za ta kiyaye ƙa’idojin aikinta cikin ƙwarewa, da kuma biyayya da kare dokar ƙasa.

Ya ce doka ce ta tanadar da matakan ladabtarwa da aka ɗauka domin tabbatar da ɗa’a da kuma ƙwarewa a tsakanin jami’an rundunar.

‘Hukuncin doka ta tanadar’

Wasu tsofaffin hafsoshin sojin da muka zanta da su, Janar Bashir Adewinbi (Ritaya) da kuma Manjo Bashir Gama (Ritaya), sun bayyana cewa hukuncin yunƙurin juyin mulki a dokar aikin soja shi ne kisa.

Sun ce babu makawa a wannan hukunci ga duk sojan da aka samu da wannan laifi, in dai ba shugaban ƙasa ne ya yi amfani da kujerarsa ya yi musu afuwa ba.

Janar Adewinbi ya ce, “Tun da binciken da aka kammala ya tabbatar cewa an yi yunƙurin hamɓarar da gwamnati, to ya zama wajibi duk wanda ke da hannu a ciki ya shirya fuskantar hukunci.

“Babu wata magana, hukuncin laifin yunƙurin juyin mulki a dokar soja kisa ne. Muddin aka sami mutum da laifin, kashe shi za a yi, kuma mun sha ganin hakan a ƙasar nan.

“Amma shugaban ƙasa yana iya amfani da alfarmarsa ya yi musu sassauci, amma idan ba haka ba, hukuncinsu kisa ne, domin ya zama darasi ga duk wani mai tunanin yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya.

“Aikin sojoji ne su kare tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, ya kamata duk wanda ya yi yunƙurin hamɓarar da gwamnati ya fuskanci hukuncin da ya dace da su a kotuna na musamman, kamar sauran masu manyan laifukan ta’addanci da dangoginsu.”

A nasa ɓangaren, Manjo Bashir Galma ya bayyana cewa ya kamata duk wanda zai shiga aikin soja ya sani cewa dokoki iri biyu ne za su yi aiki a kansa—kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma kundin dokokin aikin soji na Najeriya.

Makokar masu juyin mulki a baya

A shekarun baya an yi yunƙurin juyin mulki da dama a Najeriya, wasu sun yi nasara, wasu kuma an daƙile, inda aka kama masu hannu a ciki da suka haɗa da manyan mutane da ake zargin hannunsu.

A watan Disambar shekarar 1985, gwamnatin soji ta Janar Ibrahim Babangida ta sanar cewa ta daƙile yunƙurin juyin mulki tare da kama masu hannu a ciki, waɗanda suka hada da Manjo-Janar Mamman Vatsa.

A dalilin haka aka yanke wa hafsoshin soji 13 hukuncin kisa kan laifin cin amanar ƙasa, kuma aka harbe 10 daga cikinsu har lahira, ciki har da Manjo-Janar Vatsa a watan Maris na shekarar 1986.

A watan Yulin 1995 gwamnatin soji ta Janar Sani Abacha ta samu mutum 40 da laifin yunƙurin juyin mulki, wanda a dalilin haka aka ɗaure tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Olusegun Obasanjo a gidan yarin tare da Janar Musa ’Yar’Adua da sauransu.

Bayan shekara biyu a watan Disambar 1997 gwamnatin ta sanar da daƙile wani sabon yunƙurin juyin mulki wanda mataimakinsa, Laftanar-Kanar Oladipo Diya ya jagoranta.

An kama Janar Fit3a tare da wasu masu muƙamin Kanar-kanar guda uku da wasu manyan sojoji.

A watan Afrilun shekarar 2004, zaɓaɓɓiyar gwamnatin Obasanjo ta sanar da tsare wasu sojoji, ciki har da Manjo Hamza Al-Mustapha—Babban Dogarin Abacha—bisa zargin yunƙurin juyin mulki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *