Uba Sani Zai Gina Tashar Mota Mafi Girma Da Zamanantarwa A NIjeriya

[ad_1]

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ce gwamnatinsa za ta gina babbar tashar motocin bas mafi girma ta zirga-zirga tsakanin jihohin Nijeriya, dangane da girma da kayayyakin more rayuwa na zamani.

A yayin bikin ƙaddamar da ginin tashar a ranar Lahadi, Gwamna Sani, ya ce, tashar za ta laƙume hekta 20 a babban titi na gabashin birnin jihar a yankin Karamar Hukumar Chikun.

  • Yawan Kudaden Da Baki Suka Kashe A Sin Ya Karu A Shekarar Bara
  • Ana Hasashen Haihuwar Jarirai Har 700,000 Cikin 2026 A Kano

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Tashar Motar ta zirga-zirga tsakanin Jihohi ta zamani, tana da ƙarfin ɗaukar motoci sama da 5,000, tare da tsari mai kyau na zamani.

Gwamna Uba Sani ya ci gaba da cewa, “Tashar za ta ƙunshi dogon bene mai amfani da na’urar hawa bene, domin tallafawa tsofaffi da nakasassu.”

Bugu da kari, “Za a gina gidan man fetur, dizal, da iskar gas na mota (CNG), wanda hakan zai sanya Jihar Kaduna a sahun gaba wajen ƙirƙirar hanyoyin sufuri masu dorewa”.

Har ila yau, “Za a gina ‘three-star’ Otal a cikin tashar domin kula da matafiya, direbobi, da baƙi,” in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *