Sojoji Sun Kama Tsohuwa Mai Shekaru 65 Bisa Zargin Safarar Ƙwayoyi Ga Ƴan Boko Haram
[ad_1]
Sojojin Rundunar Haɗin Gwuiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HAƊIN KAI, sun kama wata mata mai shekaru 65, Hauwa Abulazeez, bisa zargin samar da haramtattun ƙwayoyi ga ƴan Boko Haram da ke aiki a wasu sassan Jihar Borno. Kamen ya gudana ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, a ƙaramar hukumar Askira Uba, bayan samun sahihan bayanan sirri, a cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana Hauwa a matsayin “ɗaya daga cikin manyan masu samar da tabar wiwi (cannabis sativa) ga ƴan ta’adda,” tana kuma rarraba kayan a yankunan Askira Uba da makwabtan ƙauyuka kamar Rumirgo, da Gwahi, da Wamdiyo, da Uvu da Gaya. Rundunar ta ce ana kallon ta a matsayin muhimmin ginshiƙi a da’irar masu safarar haramtattun ƙwayoyi a faɗin waɗannan al’ummomi.
- Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Munzir, Sun Kama Wasu 34 A Borno
- Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram 2, Sun Kama Wasu 8 A Borno
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Hauwa na samo ƙwayoyin ne daga ƙaramar hukumar Sarti Baruwa a Jihar Taraba, sannan tana bi ta hanyoyin da aka riga aka tanada wajen shigar da su zuwa Borno domin rarrabawa. A yayin aikin da aka gudanar ƙarƙashin Operation Desert Sanity V, Sojoji sun ƙwato buhuna 14 na tabar wiwi da aka matse, masu nauyin kimanin kilo 30 gaba ɗaya.
Rundunar ta ce ana ci gaba da tsare wadda ake zargi domin zurfafa bincike, tare da bin sawun sauran mutanen da ke cikin wannan hanyar safarar ƙwayoyi. Ta jaddada cewa katse hanyoyin samar da haramtattun kayab zai taimaka wajen rage ƙarfin ayyukan ta’addanci, tare da ƙara tsaro da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.
[ad_2]
Source link