Me Ya Sa “Tattaunawa Da Sin” Ta Kasance Ra’ayin Bai Daya Na Kasa Da Kasa

[ad_1]

Kwanan baya, kasashe daban daban sun sha tattaunawa da kasar Sin. Kimanin kwanaki goma da suka wuce, firaministan Kanada Mark Carney ya ziyarci kasar Sin a hukumance, inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan takardu masu yawa na hadin gwiwa. Bayan haka ba da dadewa ba, a Taron Dandalin Tattaunawa Kan Tattalin Arzikin Duniya (WEF) na shekara ta 2026 da aka gudanar a Davos na Switzerland, mahalarta taron sun tattauna sosai kan “Damammakin da Sin ke samarwa”, suna ganin cewa tattaunawa da Sin ya fi muhimmanci fiye da kowane lokaci a baya. Tun daga ranar 25 ga watan nan, firaministan Finland Petteri Orpo ya jagoranci tawaga mai yawan manyan jami’an kamfanoni domin ziyartar kasar Sin, hakan ya bayyana fatansa sosai na zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Me ya sa al’ummar duniya ke mayar da hankulansu kan kasar Sin?

Bari mu ba da misali da taron dandalin Davos da aka rufe ba da jimawa ba, rahoton da aka bayar kafin bude taron ya bayyana kai tsaye cewa, fito na fito kan tattalin arziki tsakanin yankuna daban daban ya kasance hadari mai tsanani dake gaban komai a shekarar 2026. Tsayawa tsayin daka kan goyon bayan ciniki cikin ’yanci, da kiyaye tsarin cudanyar bangarori da dama, da cimma nasara tare ta hanyar hadin gwiwa, da mutunta juna da kuma gudanar da tattaunawa bisa adalci da girmama juna, wadannan manufofin guda hudu da kasar Sin ta gabatar a yayin taron, sun ba da tabbacin da ake bukata kwarai da gaske ga wannan duniyar da ke fuskantar tashin hankali, kuma sun sa al’ummar duniya ta kara fahimtar cewa, kasar Sin abokiya ce amintacciya, kuma mai bude kofarta ga kasa da kasa.

A lokaci guda, tattalin arzikin kasar Sin da ya bayar da kwarin gwiwa da kuzari daidai gwargwado ga tattalin arzikin duniya mara karfin farfadowa. A shekarar 2025, a karo na farko GDPn kasar Sin ya haura zuwa sabon matsayi na RMB triliyan 140, wanda ya karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024, kuma har yanzu dai shi ne babban karfin da ke inganta karuwar tattalin arzikin duniya. Abun da ya fi muhimmanci shi ne, kasar na kara bude kofa ga kasashen waje, da more nasarorin da ta cimma sakamakon ci gaba mai inganci, tare da kasa da kasa.

Za a iya sa ran cewa, a sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta kara ba da kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma za ta ci gaba da zama “abokiya amintacciya kuma mai bude kofarta.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *