Gwamna Yusuf: “Allah Ne Ya Sanya Ni Gwamna, Muradun Kano Ne Gaba, Ba Biyayya Ga Wani Ba”
[ad_1]
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ce, Allah ne ya sanya shi ya zama Gwamna, ba wani ɗan siyasa ko mutum ba, yana mai jaddada cewa, muradun Kano ne gabansa ba muradin wani ɗan siyasa ba.
Yusuf ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake bayar da kyautar babura ga masu taimaka masa a harkokin yaɗa labaransa a shafukan sada zumunta, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce game da komawarsa Jam’iyyar APC.
“A shekarar 2023, Allah ne ya ba ni mulki, ba kowa ba, kuma har yanzu ina masa godiya da yabo a matsayin wanda zai ci gaba da taimaka mini in ci gaba a shekarar 2027,” in ji gwamnan.
Ya katse hanzari da cewa, fara tattauna batu game da babban zaɓen 2027 da ke tafe, a matsayin abu mai karkatar da alƙiblar ci gaba da ayyukan haɓaka ci gaban jihar Kano.
[ad_2]
Source link