Jihar Gombe Ta Kafa Kwamitin Sasanta Rikicin Manoma Da Makiyaya

[ad_1]

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ce gwamnatinsa ta samar da cikakken tsari na musamman, wanda aka rubuta a cikin ‘White Paper’, domin daƙile rikice-rikicen manoma da makiyaya, ’yian bindiga da sauran ƙalubalen tsaro masu alaƙa da su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da wani babban kwamitin aiwatar da White Paper kan wuraren kiwo, gandun daji da wuraren ajiyar namun daji, da kuma hanyoyin shanu a jihar.

Kwamitin ya ƙunshi ƙwararru a fannin tsaro, lauyoyi da masana fasahar taswira, kuma an ɗora musu alhakin fassara manufofin gwamnati zuwa ayyuka na zahiri da za a iya aiwatarwa da kuma tilastawa bin doka.

  • Gwamnan Gombe Ya Yi Ta’aziyyar Mutane 5 Da Suka Rasu A Hatsarin Mota
  • Yadda Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan ‘Yan Jarida 7 A Gombe

Gwamnan ya bayyana cewa kafa kwamitin ya biyo bayan aikin wani kwamitin tantancewa da gwamnatinsa ta kafa tun da farko, wanda ya duba matsalolin da ke tattare da wuraren kiwo, gandun daji da wuraren ajiyar namun daji, da kuma hanyoyin shanu, da nufin samar da hanyoyin warware matsalolin da za su kasance masu amfani kuma masu ɗorewa.

Sakamakon bincike da shawarwarin kwamitin tantancewar sun samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Jihar, sannan aka fayyace su a cikin White Paper.

A cewar gwamnan, wannan shiri na da nufin kawar da tsofaffin hanyoyin kiwo marasa tsari, ƙarfafa tsaro da tsarin doka, da kuma hana rikice-rikicen manoma da makiyaya, tare da tabbatar da wadatar abinci da zaman lafiya da jituwa a faɗin jihar.

“Xaya daga cikin manyan matsalolin da ke ci gaba da addabar Arewacin Nijeriya, har ma da ƙasar baki ɗaya, shi ne rikice-rikicen manoma da makiyaya da ke faruwa akai-akai, wanda yawanci ke samo asali daga taƙaddama kan ƙasa da albarkatu, musamman a lokacin girbi,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, “Mamaye wuraren kiwo, gandun daji da hanyoyin shanu ya ƙara tsananta lamarin, kuma gazawar gwamnatoci da suka gabata wajen magance wannan matsala da irin ƙarfin siyasar da ya dace ba abin takaici kaɗai ba ne, abin Allah-wadai ne.”

Yahaya ya bayyana cewa duk da yawaitar al’ummar Nijeriya cikin sauri, akwai faɗaɗɗun ƙasashe masu yawa da har yanzu ba a noma su ba kuma ba a amfani da su yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa ana iya amfani da irin waɗannan albarkatu yadda ya dace domin zamanantar da kiwon dabbobi, taƙaita kiwo a wuri guda, da kuma kawo ƙarshen dogon yawo da shanu ke yi wanda ke haddasa matsalolin tsaro, ’yan bindiga da garkuwa da mutane.

Ya kuma bayyana cewa ƙudurin gwamnatinsa na dawo da wuraren kiwo, gandun daji da hanyoyin shanu da aka rasa ko aka mamaye na daga cikin muhimman hanyoyin rage rikici da kare rayuwar manoma da makiyaya.

Da yake nuna cewa sama da kashi 80 cikin 100 na al’ummar jihar na dogaro da noma da kiwon dabbobi, gwamnan ya ce ya zama dole gwamnati ta nuna ƙarfin siyasa domin kare rayuka, dukiyoyi da kuma bunƙasar tattalin arziki.

Yahaya, wanda shi ne kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa rungumar hanyoyin kiwo na zamani da kuma kawar da tsofaffin hanyoyin kiwon dabbobi za su samar da sabon tsari ba ga Jihar Gombe kaɗai ba, har ma ga Arewacin Nijeriya da ƙasar baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *