Yadda Aka Gudanar Da Gangamin ‘Detty December’ Na ‘Malta Guinness’ A Enugu Da Kaduna
An Sauya Ma’anar Detty December: Malta Guinness Ta Maida Enugu da Kaduna Wuraren Kirkira da Wasanni
Detty December na da ma’ana ne na tsawon lokuta a zukata, kwarewa da suka wuce abubuwan da suka shafi kida kawai, har lamarin ya kai ga kama zuciyar al’adun matasa.
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar Guinea Da Switzerland
- Gwamnatin Zamfara Ta Ɓullo Da Shirin Amfana Da Ma’adanai Ga Al’umma Jihar
A Enugu da Kaduna, wani taro ya fice a fagen kirkira, hadin kan al’umma, da bayyana kai a matsayin gaskiya: wato Malta Guinness City Fest.
Malta Guinness ya tsara bikin cikin tsanaki, inda ya maida biranen biyu wuraren da ke cike da nishadi da fasaha, kayan ado, kida da farin ciki na bai-daya, tare da sake nuna fasahar matasan Nijeriya.
A lokacin da baki suka halarci wurare taron, sun tabbatar da cewa wannan ba taro ne da aka saba yin a kowane lokaci ne.
Yanayin tsarin wurin taron an kawata shi da fitilu masu cike da launuka, sauti mao sa kuzari, an tsara shi cikin hikima domin gayyatar matasa domin su yi bincike, su hadu da juna, kuma su bayyana kansu cikin ‘yanci.
Zane-zanen da aka kawata surin da su sun yi nuni da karfafa kirkira mai karfafa hali, nune-nunen kayan ado sun nuna salo, yayin da abubuwan sha na Malta Guinness marasa giya masu wadatar sinadarai suka kasance cikakun kari ga yanayin dake cike da kuzarim
A tsakiyar Malta Guinness City Fest, akwai abubuwa masu karfi da aka tanada wajen karfafawa matasa. Kafin taron, Malta Guinness ta shelanta shiga gasar nuna baiwa, inda ta bai wa masu fasahar kirkira masu tasowa wata dama ta musamman domin nuna basirarsu a babban dandali.
Sakamakon da aka samu ya wuce abin aka yi tsammani, inda dandalin ya cika da nune-nunen abubuwan baiwa na musamman, kirkira, da kwazo. Ladaddakin da aka bayar sun yi daidai da girman burin fa aka cimma, domin wanda ya zo na farko ya samu Naira 500,000, yayin da na biyu da na uku suka samu Naira 400,000 da Naira 300,000 bi-da-bi, abin da ke nuna kwazon kamfanin wajen saka hannun jari a cikin burin matasan Nijeriya a sarari.
Yayin da yamma ta yi karatowa, City Fest ta kai kololuwar nishadinta. Ayyuka masu daukar hankali daga Ice Prince, Crayon, Runtown, MIA, DJ Dewik, Hypeman Best, da sauran fitattun mawaka sun maida wurin taro wurin da za a motsa da annashuwa. Kowanne aikin ya kara karfafa asalin bikin: wuri ne da ake murnar baje baiwa da fasaha, kara karfin murya, da sanya kirkira a cikin hankali akan dandamalin waka.
Baya ga kida, kwarewar bikin ya bazu zuwa wurare da aka tsara domin karfafa hadin kai da tuno abubuwan baya. Wasanni kamar Ludo, Snakes and Ladders, da Twister sun sanya rafin ciki a zukatan baki, inda aka samar da dariya da mu’amala mai cike da annashuwa a tsakanin bakin da ba su san juna ba, amma sannu a kankanin lokaci suka zama abokai. Abin da ya fi jan hankali shi ne yanayin daukar hoto da ya zama abin ya nishadantar da jama’a,
Da yake magana kan hangen nesa da ke bayan bikin, Manajan kayayyakin Malta Guinness, Rahmotallahi Adeniyi, ya ce:
“Malta Guinness City Fest hanyar mu a fannin kirkirar lokuta na gaskiya ga matasa, lokuta inda ake karfafa kirkira, ana murnar bambancin mutum, kuma hadin kai yana da ma’ana.”
Alherin da Malta Guinness, ya kawo ba wai ya tsaya ga abin sha kawai bane; har ma nufin yadda muke shiga cikin al’adu da tallafawa bayyana kai a hanyoyi da ke da ma’ana sosai.
Wannan ma’anar ta bayyana a ko’ina a Malta Guinness City Fest. Daga masu kirkira da masu kafa salo, zuwa masoya kade-kade da masu sha’awar al’adu, baki sun bayyana kansu, suna nuna kansu ta hanyar salo, motsi, da tattaunawa.
Bikin ya zama madubi mai rai na ruhin alamar Malta Guinness: gaskiya, cike da armashi, kuma da zurfin hadin kai da al’adun matasa.
Ta hanyar kawo Malta Guinness City Fest zuwa Enugu da Kaduna, kayayyakin sun sake tabbatar da jajircewarta wajen hada kowa da kowa da dacewa da al’adu, tana tabbatar da cewa kwarewar Detty December ba ta tsaya ga birni daya ko wani rukuni na masu sauraro ba. Maimakon haka, an raba shi, an dasa shi cikin al’umma, kuma an ci gaba da yi ta hanyar kirkira.
‘
Ba ga taro kadai ba, Malta Guinness City Fest wata kakkarfar sanarwa ce. Mai nuna gaskiya ta bunkasa inda ake ba kirkira fili, inda muryoyin matasa ke jin karfi, kuma inda mutane ke da ‘yancin kasancewa da kansu.
Yayin da tarihin Detty December ke ci gaba da bayyana, abu daya ya tabbata: Malta Guinness ba kawai ta shirya bikin kawai ba har ma ta kirkiri wata kwarewa da za a rike a zuciya har bayan karshen wannan lokaci.
Ga hotunan yadda gangamin ya gudana:





