Sadio Mane: Daga Ƙwallon Cikin Unguwa Zuwa Zakaran Afirka


Wannan shi ne karo na biyu da ɗan wasa Sadio Mane ya sake jan ragamar tawagar Senegal zuwa lashe gasar AFCON, amma a wannan karon, ba lashe gasar ba ce kawai ke jan hankali.

Mane, wanda tsohon ɗan wasan Liverpool da Bayern Munich ne, ya lashe gasar AFCON karo na biyu tare da tawagar Senegal, bayan doke Morocco mai masaukin baƙi a wasan da ya haifar da cece-kuce.

Duk wanda ya kalli wasan ƙarshen, ana kusa da tashi wasa ne kocin Senegal Pape Thiaw ya buƙaci ƴan wasansa su fice daga filin wasan bayan da alƙalin wasan ya ba Morocco bugun fanareti a minti na 98 da wasan bayan ɗan wasan baya Senegal El Hadji Malick Douf ya ja Brahim Diaz ya faɗi ƙasa.

  • AFCON 2025: CAF Ta Ci Tarar Algeria, Ta Dakatar Da Ƴan Wasanta
  • Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025

Amma a lokacin da ƴan wasan Senegal ke ƙoƙarin ficewa ne aka ga ɗan wasa Sadio Mane yana ta ƙoƙarin lallava su da su koma cikin fili su ci gaba da buga wasan tare da taimakon mai tsaron ragar ƙungiyar, Edourd Mendy.

Kimanin minti 16 bayan lamarin ne Diaz ya buga fanaretin da salon panenka, amma ya zubar, inda Mendy ya kama ƙwallon cikin sauƙi. Bayan an tashi babu ci ne aka shiga ƙarin lokaci, inda Pape Gueye ya zura ƙwallon da ta zama sanadiyar samun nasarar Senegal a kan Morocco mai masaukin baƙi.

Xan wasa Mane, wanda ya ce wannan gasar AFCON ta ƙarshe da zai buga, ya nuna bajinta da shugabanci a lokacin da ake buƙata, musamman inda ƴan wasan tawagar suka buƙaci ya wakilce su wajen ɗaga kofi duk da ba shi ba ne kyaftin.

Bayan tashi daga wasan Mane ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa tana da muhimmanci, kuma duniya na kallonmu. Don haka bai kamata mu zama sanadiyyar vata harkar a idon duniya ba.

Yaushe Mane Ya Fara Ƙwallo a Senegal?

Sadio Mane ya fara buga ƙwallo ne daga garin Bambali, gari da ke kudu maso yammacin Senegal, inda ya fara ƙwallo a layi a filin turvaya, sannan yana ɗan shekara 13. Mane, wanda yanzu yake buga wasa da ƙungiyar Al-Nassr a Saudiyya, ya samu nasarori da dama, amma duk da haka bai tava mantawa da asalinsa ba.

Yana da ɗimbin masoya a Bambali saboda kyautarsa da ƙoƙarin da yake yi wajen ginawa da gyara asibitoci da makarantu da gina masallatai da ma tallafin da ya bayar a lokacin annobar Korona.

Ƴan uwa da dangi kuma sun bayyana shi a matsayin “wanda yake aiki domin kowa, kuma Musulmin kirki. Haka kuma ya nuna hali na daban a lokacin da yake ƙwallo a Ingila, inda da ya riƙa wanke ban-ɗakunan masallacin Toɗteeth.

Mane ya buga wa Senegal wasa sau 120, inda ya zura ƙwallo 53. Yana nuna ƙwarewa matuƙa a filin wasa, sannan yana da burin wakiltar ƙasarsa a gasar cin kofin duniya da za a buga a bana, inda yake fatan ƙara kafa tarihi.

Ya varar da bugun fanareti a farkon wasan ƙarshe a gasar AFCON ta 2021, amma kuma ya samu nasarar zura bugun fanareti na ƙarshe, inda Ƙasarsa ta lashe gasar ta hanyar doke Masar a birnin Yaounde.

Bayan haka ya kuma jagorancin ƙasarsa wajen doke Masar a wasan cike-gurbi zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga a Ƙatar, duk da raunin da ya ji ya hana shi buga gasar.

Duk da cewa Mane ba mutum ba ne mai son girma, kuma ba shi ba ne kyaftin, amma idan ya yi magana, abokan wasansa suna sauraro. A jawabinsa na kafin wasansu da Masar, ya ƙarfafa musu gwiwa. Mane, wanda ya yi zamani ne sosai tare da tsohon kocin tawagar, Aliou Cisse, wanda ya jagoranci tawagar ƙasar tsakanin 2015 zuwa 2024, amma kocin ƙasar na yanzu, Pape Thiaw na da burin ganin ɗan wasan ya ci gaba da wakiltar ƙasar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *