Buƙatar Magance Kisan Kiyashi Da Ƴan Bindiga Suka Yi A Kasuwar Neja
A watan Janairun 2026 ne, wasu ƴan bindiga, suka kutsa cikin babbar kasuwar Daji, da ke a jihar Neja, inda suka yiwa mutane, sama da 40, kisan gilla.
Wannan mummunan ta’addacin dai, ya nuna a zahiri, irin yanayin lamarin ƙalubalen rashin tsaro, da ƙasar ke ci gaba da fuskanta.
Duk da yawan shelar da gwamnati ke ci gaba da yi na cewa, tana ci gaba da ɗaukar matakai, domin lalubo da mafita kan wannan matsalar, amma ana kuma, ƴan bindiga da kuma ƴan ta’adda, na ci gaba da ɗaukar rayukan alummar, da ba su ji, ba su kuma gani ba.
- AFCON 2025: Zan Taimaka Wa Uganda Ta Doke Super Eagles Duk Da Mahaifina Ɗan Nijeriya Ne – Ikpeazu
- Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Tinubu
Lamarin ka hallaka mutane, ba gari ba sabat, kusan za a iya cewa, sai ƙara zamowa yake yi runwan dare, a ƙasar, inda hakan ke ci gaba da yin hannun riga, na iƙirarin gwamnatin, na shawo kan matsalar.
Akasarin ƴan Nijeriya dai, na da yaƙin cewa, batun ƙoƙarin na gwamnati kan shawo kan matsalar, a fatar baki ne kawai.
Babban abin takaicin shi, da tsakiyar rana ne, ƴan bindigar, suka kutsa cikin kasuwar, suka ƙaddamar da aika-aikar tasu, ta hanyar yin amfani da muggan makamai.
Harin na jihar Neja, ya dai kasance, tamkar a cikin film ɗin ban tsaro, inda maharani, suka ɗaure waɗanda lamarin ya rutsa da su, suka kuma yiwa aƙalla ƴan kasuwa 30, yankan Rago, suka kuma shiga cikin wasu yankuna suka buɗe wuta suka kashe wasu a yankin, tare da cinnawa wasu gidaje wuta.
Shin ya za a ce, waɗannan marasa imanin har suka kammala aikata ta’asarsu, ba tare da jami’an tsaro, sun kawo ɗauki ba?
Kazalika, shin wasu daga cikin mazuna yankin sun yi gaggawar kai rahoton haring a ofishin ƴansanda mafi kusa?
Ya ya matsayin batun tura jami’an tsaro zuwa yankin, tun bayan aukuwar harin da ƴanbinda suka kai a makarantar Papiri?
Duk da cewa, ƙasar nan, ba wai tana a cikin yanayi na yaƙi bane, amma mai ya sa, mutane ba su iya yawo salin alin a cikin ƙasar ko kuma zuwa kasuwa, amma sai sun fuskanci matsalar tsaro?
Daga cikin waɗanda maharani suka hallaka, har da yara, ba tare da sun akita wani laifi ba.
Wasu mazauna yankin sun ce, maharan, sun yiwa kasuwar ƙawanya ne biyan sun fito daga mavoyarsu da ke a jejin Kainji National Park, inda hakan, nuna cewa, mavoyar ta su, dama can sananniya ce.
Idan har malafar ta su, a cikin jama’a take, shin me ya haɗa jami’an tsaron tarwatsa su, daga sansannin na su?
Nisan da ke daga kasuwar zuwa yankin Papiri na ƙaramar hukumar Agwara, inda aka sace ɗalibai sama da 200, a ranar 21 ga watan Nuwambar 2025, na makarantar St. Mary’s Catholic , bai da wata nisa.
Hakan dai, ya nuna irin gazawar gwamnati na magance ƙalubalen rashin tsaro a jihar.
Lamarin dai, na ci gaba da haifar da shakku a zukatan jama’a, duba da yadda maharan, suka kutsa cikin kasuwar suka kuma kci Karensu, babu babbaka, tare da satar kayan abinci da kaya masu tsada,
Jihar dai, ta jima tana fusknatan hare-haren ƴan bindiga, inda akasari, gwamnati kawai ke fitar da sanarwar, yin tir da duk wani hari da aka kai.
Bugu da ƙari, bayan kai harin na kasuwar Dajin shugaba Bola Tinubu, ya fitar da sanawar tin tir, da kai harin, tare da umartar jami’an tsaro da su kamo maharani da kuma kuvutar da waɗanda maharani suka sace.
Mun dai faɗa cewa, akwai buƙatar gwamnati, ta ƙara ƙarfafa magance matsalar ta rashin tsaro, a ɗaukacin faɗin ƙasar.
Idan da za tambayi ƴan Nijeriya me suka fi buƙata a tsakanin samar masu da ababen more rayuwa da tsaro, tabbas, za su ce, sun fi buƙatar a samar masu da tsaro.
Wannan Jaridar, na jajatanwa iyalai da kuma ƴan uwan waɗanda lamarin, ya rutsa da su, a harin na kasuwar, inda kuma waɗanda suka samu raunuka, muke masu fatan Allah ya ba su lafiya Ya zama wajibi, gwamatin ta tashi haiƙan domin samar da tsaro a ɗaukacin faɗin ƙasar, tun kafin lokaci ya ƙure.