Babban Taron APC: Ƙungiyar Masu Ruwa Da Tsaki Ta Amince Da Yilwatda
A shirye-shiryen babban taron jam’iyyar APC mai mulki na kasa a ranar 28 ga Maris, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun amince da jagorancin shugaban jam’iyyar na yanzu, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Kungiyar masu ruwa da tsaki ta APC, wacce ta sanar da amincewa da shi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ta nemi Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar, da Shugaba Bola Tinubu, da dattawan jam’iyyar, da dukkan masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da tsarin shiyya-shiyya da ake da shi yanzu don tabbatar da hadin kai, daidaito, da adalci.
- Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Kisan Kudirat Abiola, Ta Sallami Al-Mustapha
- Babakeren Amurka: Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi
Yilwatda daga Jihar Filato (Arewa ta Tsakiya) ya zama Shugaban Jam’iyyar APC ta Ƙasa a lokacin taron NEC na jam’iyyar a ranar 24 ga Yuli, 2025, wanda masu lura da siyasa suka ɗauka a matsayin wani mataki na mayar da wannan matsayi zuwa tsarin shiyya-shiyya inda yake a da kafin zaɓen Dr. Abdullahi Ganduje (Arewa maso Yamma) tsakanin 3 ga Agusta, 2023 da 27 ga Yuni, 2025.
A jawabinsa, shugaban taron, Dr. Dominic Alancha ya ce, a ƙarƙashin jagorancin Yilwatda, jam’iyyar ta sami kwanciyar hankali, fahimtar juna a rikicin cikin gida, gudanar da tsarin jam’iyya da kuma sake tsara manufofi don samun nasarar zaɓe a nan gaba.
Ya ce, zaɓen shugaba a tsarin shiyya-shiyya, itace hanya mafi dacewa, wacce al’amura ke daidaituwa, da kuma jin daɗin kasancewa tare da ɓangarori daban-daban na jam’iyyar, don haka, akwai buƙatar ci gaba da tsare-tsaren da ake da su a yanzu.