Gwmantin Kaduna Ta Tabbatar Da Sace Masu Ibada 177 A Kajuru

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ayyana garin Rijana da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna a karamar hukumar Kachia ta Jihar a matsayin cibiyar ‘yan ta’adda a Nijeriya.

In ba a manta ba, Tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a lokacin gwamnatinsa ya gabatar da shawarar sauyawa mazauna garin Rijana matsuguni saboda ta zama maɓoyar ‘yan ta’adda.

  • Darajar Tamburan Kasar Sin Sun Karu A Duniya
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 2, Sun Ceto Mutane 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi Da Zamfara

Da yake jawabi a lokacin ziyararsa a garin Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru inda ake zargin ‘yan bindiga sun sace masu ibada 177 daga coci uku a ranar Lahadi da ta gabata yayin ibada, Gwamna Sani ya tabbatar wa al’ummar cewa, za a dawo da mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya, duk da cewa ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soja a Kurmin Wali ganin kusancinsa da Rijana.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ‘yansandan jihar sun musanta rahoton sace masu ibadar, har sai a ranar Talata, lokacin da aka fitar da sunayen waɗanda ibtila’in ya shafa su 177.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *