AFCON 2025: Lookman Da Osimhen Na Daga Cikin Zaratan Yan Wasa 11 Na Bana
[ad_1]
Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta fitar da sunayen zaratan ‘yan wasa 11 da suka fi ƙoƙari a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirika (AFCON) da aka kammala a kasar Morocco, inda sunayen ‘yan wasan Nijeriya 3 da suka hada da Victor Osimhen, Ademola Lookman da Calvin Bassey suka fito a cikin jerin sunayen na bana.
Jerin sunayen ya kunshi ‘yan wasa daga kasashen da suka taka rawa a gasar da aka kammala amma kuma sunayen yan Nijeriya, Senegal, da Morocco ne suka mamaye jadawalin, an fitar da sunayen yau Laraba, kwana uku kacal bayan kammala gasar.
Osimhen ya buga wasanni shida daga cikin 7 da Super Eagles ta buga a bana, wasan neman matsayi na 3 wanda Nijeriya ta doke kasar Masar ne kadai wasan da Osimhen bai buga ba, ɗan wasan na Galatasaray ya zura kwallaye hudu a gasar ta bana.
Ademola Lookman dake taka leda a Atalanta ya zura kwallaye 3 kuma ya taimaka wajen zura 3 a wasannin da ya buga yayin da Calvin Bassey na Fulham shi ma ya samu gurbi a jadawalin bayan kokarin da ya yi wajen tsare bayan Super Eagles.
Ga cikakken jerin zaratan ‘yan wasa 11 na gasar AFCON ta bana.
Mai tsaron raga:
Yassine Bounou (Maroko)
Masu tsaron baya:
Achraf Hakimi (Maroko)
Moussa Niakhat (Senegal)
Calvin Bassey (Nijeriya)
Noussair Mazraoui (Morocco)
‘Yan wasan tsakiya:
Ademola Lookman (Nigeria)
Pape Gueye (Senegal)
Hydrissa Guee (Sengal)
‘Yan wasan gaba:
Brahim Díaz (Marocco)
Victor Osimhen (Nijeriya)
Sadio Mane (Senegal)
[ad_2]
Source link