Jama’a Sun Nuna Rashin Gamsuwa Da Donald Trump Yayin Da Ya Cika Shekara Guda a Wa’adin Mulkinsa

[ad_1]

A lokacin bikin cika shekara guda na wa’adin mulkin gwamnatin Amurka ta yanzu, binciken jin ra’ayoyin jama’a na duniya da kafar ta gudanar ya nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna rashin gamsuwa sosai game da aikin gwamnatin Amurka ta yanzu a harkokin cikin gida da na waje, tare da bayyana karancin gamsuwa ga matakan da gwamnatin ke dauka a fannoni da dama a cikin shekara guda.

A ranar 17 ga watan Janairu, CGTN ta kaddamar da binciken jin ra’ayoyin jama’a ga masu amfani da intanet na duniya, wanda aka gabatar a dandamali na harsuna 5 a CGTN, inda lamarin ya ja hankalin jama’a 16,990 cikin sa’o’i 24 wadanda suka kada kuri’a da bayyana ra’ayoyinsu. Binciken ya nuna cewa, kashi 84 cikin 100 na wadanda suka shiga binciken sun nuna rashin gamsuwa sosai game da mulkin gwamnatin Amurka ta yanzu. Kashi 86.2 cikin 100 sun yi Allah wadai da manufofin harkokin waje na dora “Amurka a gaba da komai”, kana kashi 89.6 cikin 100 sun yi imanin cewa Amurka ta gaza a harkokin kasa da kasa a cikin shekarar da ta gabata.

A farkon sabuwar shekara, jerin matakan cin zarafi da Amurka ta yi a Venezuela, Iran, da yankin Greenland na kasar Denmark, da sauransu bisa gaban kanta, sun sake fallasa ainihin matakin da gwamnatin kasar ke dauka, wato babakere da fin karfi, wanda ya keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin dangantakar kasa da kasa. Yana kuma kalubalantar tsarin kasa da kasa na yanzu.

A bincike na shekara ta 2025, kashi 64.7 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyinsu sun bayyana Amurka a matsayin kasar da ta fi haddasa fitinar tayar da yaki a tarihin duniya. Kashi 63.8 cikin 100 kuma sun yi imanin cewa Amurka ta lalata tsarin kasa da kasa na yanzu sosai, inda wannan adadin ya karu da kashi 9.7 cikin 100 a cikin shekara guda. Ban da wannan kuma, kashi 63.4 cikin 100 suna ganin cewa, manufofin Amurka sun riga sun yi barazana ga zaman lafiyar duniya, adadin ya karu da kashi 10.3 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *