DSS ta kama tsohon Ministan Shari’a Malami bayan fitowarsa daga gidan yari




Hukumar Tsaro ta farin Kaya (DSS) ta sake tsare tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, jim kadan bayan an sako shi daga gidan Yarin Kuje jim kadan bayan ya cika sharuddan belinsa.

Malami wanda ya kasance Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a zamanin Marigayi Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya fito daga gidan yari ne bayan kotu ta tsare shi ka zargin almundahanar kudade da Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) take zarginsa.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin tsare shi a Gidan Yarin Kuje ne EFCC kan zargin safarar kudaden haram a zamanin jagorancinsa a ma’ikatar shari’a daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Gabanin bayar da belinsa a kan Naira miliyan 500, Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta tsare tsohon ministan tare da matarsa da dansa a Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja daga watan Dismabar 2025 zuwa farkon watan nan na Janairu 2026.

Kowannensu an bayar da belinsa a kan Naira miliyan 500 bayan sun musanta zargin da Hukumar EFCC take tuhumar su a kai.

Karin bayani na tafe.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *