Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya Nuna Alhini Kan Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6 A Kano
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan kisan gilla da aka yi wa wata baiwar Allah tare da ’ya’yanta shida a Jihar Kano.
A wata sanarwa da ya fitar, Dakta Yero, wanda shi ne Dallatun Zazzau, ya ce lamarin abin tausayi ne ƙwarai da gaske, inda wasu ’yan gari suka shiga har makwancin wata baiwar Allah a Unguwar Dorayi Charanchi, Kano, suka hallaka ta tare da ’ya’yanta guda shida, lamarin da ya faru a ranar Asabar, 17 ga Janairu, 2026.
- Ƴan Nijeriya Sun Cire Tiriliyan ₦36.3 Ta ATM Cikin Watanni 6 Duk Da Ƙarin Kuɗin Caji — CBN
- Sojoji Sun Daƙile Harin Jirgi Maras Matuƙi Na Ƴan Boko Haram A Borno
Ya bayyana cewa abin takaici ne ace ana samun irin wannan mummunar aika-aika a cikin al’umma mai albarka, yana mai jaddada cewa babu wani addini da ke koyar da irin wannan ta’addanci ko zalunci.
“Cikin alhini da jimami nake bayyana takaicina kan wannan mummunan lamari. Babu wani addini da ke halatta kisan rayuka marasa laifi. Wannan aiki ya saba wa koyarwar addini da ɗabi’un al’ummarmu,” in ji Dakta Yero.
Tsohon gwamnan ya yi kira ga al’umma da su ƙara tsoron Allah, su kuma kaucewa duk wani abu da zai iya kai su ga aikata mummunan aiki, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya, juna da fahimta a cikin al’umma.
Haka kuma, Dakta Yero ya yi kira ga mahukunta da hukumomin tsaro da su ɗauki dukkan matakan da suka dace domin gano tare da kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci, tare da gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace da su.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, musamman mijin marigayiyar, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamatan, Ya karɓi rayukansu a matsayin shahada, tare da bai wa iyalansu haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
“A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya ba mu aminci da salama a ƙasarmu baki ɗaya,” in ji shi.
Lamarin dai ya jefa al’ummar Kano da ma ƙasar baki ɗaya cikin alhini, inda jama’a da dama ke kira da a tabbatar an yi adalci domin hana faruwar irin wannan mummunan lamari nan gaba
[ad_2]
Source link