Jiragen Ruwa Guda 32 Ɗauke Da Kaya Sun Sauka A Tashar Jihar Legas


Hukumar Kula da Tashohin Jiragen Ruwa ta Ƙasa, NPA ta bayyana cewa, Jiragen Ruwa guda 32 ɗauke da kaya da suka haɗa da Man Fetur da abinci da sauransu, sun suka a Tashar Jiragen Ruwa da ke a jihar Legas.

Hakan na ƙunshe ne, a cikin wata sanarwa da Hukumar  ta saba fitarwa a duk kullum, inda sanarwar ta ce, kayan su sauka ne a Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa,Tin-Can Island da ke a Lekki.

  • Tsarin ‘Digital Call-Up’ Ta NPA Ya Samu Karɓuwa A Tashar Jiragen Ruwa Na Onne
  • Yadda Tsare-tsaren Tinubu Na Fitar Da Kaya Ketare Suka Ƙara Wa NPA Ƙwarin Guiwa

Sanarwar wadda Hukumar ta fitar a ranar Litinin ta ce, Jiragen ruwan sun sauka a waɗannan Tashohin ne, da kaya iri da bana da ban da suka yo jigilrasu, zuwa cikin ƙasar nan.

A cewar sanarwar, kayan sun haɗa da, Ɗanyen Mai, Man Jirgin sama, sanadarin haɗa Kwalta da kwantaina da Takin zamani da sauransu.

Hukumar ta ƙara da cewa, tuni wasu Jiragen Ruwa guda 10, sun sauka a Tashohin, inda Hukumar ta ce, Jiragen na ɗauke da kaya kamar su Man Dizil, Ɗanyen Mai Alkama da sauransu.

A  cewar Hukumr ayyukan da ake gudanarwa a waɗannan Tashoshin, na ci gaba da guda, musamman duba da cewa, ana ci gaba da yin ƙoƙari domin Jiragen sun sauka, ba tare da wata matsala ba.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *