’Yan sanda sun kama mutane 41 a ‘gidan yanan kai’ a Binuwai




’Yan sandan sun gano wuni ɓoyayyen wuri da suke zargin ana yanka mutane, inda ta kama mutane 41 a Makurdi hedikwatar  Jihar Binuwai.

Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya sanar da Aminiya cewa  “An gani wani gida da ake zargin ana yanka mutane ana fawar namansu a unguwar Wurkum da ke birnin jihar.”

Bayani da wakilinmu ya samu ya nuna asirin gidan yanan kan ya toni ne  bayan da suka shigar da wata mace da suka kama ta a unguwar da ke bayan ɗakin karatu a layin Awe suka shigar da ita gidan ƙarfi da yaji.

Yadda na faɗa a taron ’yan yanka kai

Wata mata da aka ceto a gidan ta bayyana yadda lamarin ya rutsa da ita bayan ta hau babur mai ƙafa uku da nufin zuwa gida daga coci.

“Na shiga Keke Napep na ce ga inda zan sauka, sai suka wuce da ni, bai tsaya ko’na ba sai wannan gidan a can nema na ga wata ’yar maƙwabcinmu da ta yi ɓatan dabo tun watan jiya, ashe tana nan gidan ita ma.”

Ta yi bayanin cewa, “Na je coci mun yi taron adduo’in shiga Sabuwar Shekara a Majami’ar (RCN) a Layin Kasuwa nan Makurɗi, bayan Mun tashi sai na ga kuɗin da ya rage min a ba zai ishe ni in ɗauki acaɓa ba zuwa gida ba.

“Sai na yanke shawarar in ɗan taba tafiya in daga hanya sai in hau Keke Napep ya kawo ni gida unguwarmu, ya ce si lallai in ba shi Naira 400 ya kawo ni gida, Layin International Market, Makurɗi.”

Ta ci gaba da cewa, Bayan mun ɗan yi tafiya sai ya ce min bari ya shiga gidan mai ya ƙara mai, na cikin tankin kaɗan ne kada ya kasa mana a hanya muna tafiya.

“Mun taɓa tafiya kaɗan, bayan ya sauya hanya ya ɗauki hanyar tititn Iyorchia Ayu, sai na  ce masa ya ya tsaya in sauka, ni ba nan zan bi ba, sai ya ƙi ya tsayawa, ya ce bari ya kirawo wani mai Keke Napep ya ɗauke ni.

“Ni duk jikina bai ba ni ba, na hau Keke na bi shi muka tafi. Yana zuwa daidai shataletale sai ya sake sauya hanya shi ma,” in ji ta.

Ta ce, “Muna zuwa wani wurin na ga ya yi cikin gida, qarshe yana kawo ni gidan,  sai na rasa kataɓus una juka Ina addua’a ana nema Naga wata yarinya ’yar maƙwabcinmu an sato ta an kawo ta gidan.”

Mun kama masu yanka mutane — ’Yan sanda

Kakakin ’yan sanda a jihar, DSP Udeme Edet, ya ce bayan da aka kawo masu rahoton ɓacewar matar da kuma inda ake zargi an kai ta, “Sai muka tura jami’anmu cikin shigar burtu zuwa wurin, inda suka yi nasarar kama mutum arba’in da ɗaya.

“Daga cikin mutanen da aka samu a gidan har da masu yanka mutanen da ma waɗanda ba a kai ga yanka su ba, da aka kuɓutar da su.

“Yanzu haka waɗanda ake zargi suna tsare ana yi musu tambayoyi,” in ji DSP Udeme Edet.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *