Gwamnatin Tarayya Ta Duƙufa Wajen Gina Ingantattun Rundunonin Tsaro

[ad_1]

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na gina
ingantattun rundunonin soji, cike da ƙwararru da kuma juriya, domin kare martabar Nijeriya da kuma tallafa wa ci gaban ƙasa.
Musa ya bayyana haka ne a ranar Litinin, a wajen buɗe taron ƙarawa juna sani na ƙasa, wanda aka shirya; domin tunawa da ranar sojojin ƙasar na shekarar 2026 a Abuja.

Ya ce, ma’aikatar tsaro a ƙarƙashin gwamnatin mai ci, tana ba da fifiko kan jin daɗin sojoji da inganta horar da su da inganta koyarwa da kuma faɗaɗa samar da tsaro na cikin gida, domin tabbatar da ɗorewar tsaro na tsawon lokaci.
A cewar tasa, ci gaba da tsare-tsare na dokoki suna farfaɗo da masana’antun tsaro na cikin gida, da ƙarfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, samar da ayyukan yi da zurfafa abubuwan cikin gida tare da rage dogaro ga masu samar da kayayyaki na ƙasashen waje.

  • Matakin Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’umma Tsakanin Sin Da Afirka Ya Dace Da Ajandar Nahiyar Ta Nan Zuwa 2063
  • An Yi Bikin Murnar Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Ta Sin Da Afirka A Afirka Ta Kudu

Musa ya bayyana cewa, Nijeriya na amfani da waɗanda suka samu ƙwarewa a cikin gida tare kuma ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire ta fuskar tsaro da kuma samar da ƙwarewa.
Ya ƙara da cewa, dandali na tsaro da aka samar a cikin gida a yanzu, ya nuna yadda cibiyar masana’antun tsaron Nijeriya ke daɗa ƙarfi da kuma irin gudunmawar da take bayarwa, wajen samar da tsaro da bunƙasar tattalin arziƙin yankin.

Game da ayyukan, ministan ya bayyana cewa; ingantacciyar hanyar horar da sojoji ta
musamman da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tare da abokan hulɗar yanki da na ƙasa da ƙasa, sun inganta musayar bayanan sirri da tasirin aiki, kan barazanar da ke tsakanin ƙasashen duniya.

Ya ƙara da cewa, ci gaba da kai hare-hare da sojoji suka yi a yankunan ƴan ta’adda
daban-daban, sun samu gagarumar nasara, yayin da ingantattun ayyukan sojan ruwa da wayar da kai kan harkokin teku ya daƙile ayyukan miyagun laifuka da kuma kare muhimman kadarorin
ƙasa.

Har ila yau, Musa ya jaddada cewa; tsaro wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, inda ya yi kira
ga al’umma, sarakunan gargajiya, malaman addini da na ƙananan hukumomi, da su ba da
goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci.

Haka zalika, ya buƙaci mahalarta taron da su samar da shawarwari masu amfani, domin ƙara ƙarfafa gine-ginen tsaron Nijeriya da kuma haɗin kan ƙasa.
Ministan, ya yaba wa shugabannin tsaron soji, bisa jajircewarsu, inda ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa; sojoji suna da azama da kuma ƙarfin da za su iya karya lagon makiya Nijeriya.
“Nijeriya babbar ƙasa ce, sannan da haɗin kai da juriya, za mu iya shawo kan ƙalubalen da
muke fuskanta da kuma samar da makoma mai inganci,” in ji shi.

Ministan, ya kuma jinjina wa jaruman da suka mutu, suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa tare da yaba wa ma’aikatan da suka yi aiki bisa jajircewa da kuma ƙwarewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *