Manzon Allah SAW Abin Kowa Ya Yi Murna Da Shi Ne
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ta’ala wa Barakatuhu. Mauludi ma’anarsa tuna haihuwar wani shugaba, wani gwarzo, wani babba, da ya kawo wani taimako a cikin ɗan-Adam gaba ɗaya ta ko wacce hanya; hanyar ilmi, hanyar cigaba, hanyar tattalin arziki, da sauransu, har ya koma zuwa ga Allah, ɗan-Adam suka yi amfani da wannan abu da ya kawo kuma suka amfana. To yana daga cikin gode masa, yana daga cikin abin da zai sa waɗanda za su zo daga baya su yi koyi dashi, a riƙa tunawa dashi ana faɗar waɗannan abubuwan da yayi.
Haka kuma Mauludi yana iya ɗaukar tuna wata rana da aka sami wani alheri a ƙasa ko a gari ko a yanki (misali: ranar samun ƴancin kai), masanan a nan Nijeriya muna yin Mauludi duk ranar 1 ga watan Oktoba saboda tunawa da ranar samun ƴancin kai namu, domin a tuna gwarazan da suka yi gwagwarmayar samo mana wannan ƴanci, domin mu fahimci meye ma yancin kai, don mu san ya za a yi mu kawo cigaba ga ƙasarmu, mu san ya za a yi mu riƙe ƙasarmu da kyau ba tare da sakaci ba. Wani misali kuma, idan an taɓa samun wani tashin hankali ko rashin zaman lafiya (Allah ya kiyaye) sai kuma daga baya aka samu yin sulhu, to wannan ranar sulhun ma za a iya kiyaye ta a riƙa tunawa da ita. Alƙur’ani ya faɗa mana cewa, bani Isra’ila sun nemi Annabi Isah AS, ya nema daga Ubangijinsa cewa, a saukar musu da abinci daga sama, ya yi musu faɗa akan cewa “me ya kai ku neman wannan? Kuna shakkar Allah ne?” Sai suka ce “A’a ba haka bane, kawai muna so muga gaskiyar ka ne!”. Sai Annabi Isah ya roƙi Allah, yace “Allah ga abin da mutane na suka faɗa, Ni dai na yi imani”. Sai al’ummar Annabi Isah ɗin suka ce masa “muna so mu riƙi wannan rana da abincin zai sauka ta zama, ‘idan li awwalina wa akhirina wa aayatan minka…, – ma’ana zamu riƙeta ranar wani taro babba (idi babba)’, Annabi Isah ya gaya ma Ubangiji, sai Allah SWT yace “to zan saukar da shi, kuma na yadda su riƙi wannan rana ranar idi, amma duk wanda ya yi butulci bayan haka zan azabtar da shi azabar da ban yi ma wani irinta ba”.
- Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah
- Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Koma APC
To in dai saukar abinci ta kai matsayin a riƙa tunawa da ita, kuma Alƙur’aninmu ne ya faƙa, har ma akwai sura mai sunan saukar abincin, “Suratul Ma’idah” to ina ga tunawa da Annabawan Allah baki ɗaya? Ina ga tunawa da shugabansu kuma cikamakon Annabawa gaba ɗaya, wanda yazo da wayewa da ƙwarewa, wanda duk abinda aka ga bai cika ba to ba daga shi ba ne SAW, daga mune wanda muka ɗauko abin, amma ba daga shi tawaya tazo ba.
An haifi Annabi SAW kamar yadda yazo, 12 ga watan Rabi’ul Auwal (mafi rinjayen riwaya), shekarar Giwa, ya yi shekara 40 sannan Allah ya aiko shi, ya yi shekara 13 a Makkah, sannan ya yi hijira, kaga yanzu idan ka ɗora waɗannan shekaru 13 akan 40 zaka ga ya zama 53 kenan, to mun fara tarihi da kalandar mu ta hijira, yau hijira tana 1447, idan ka haɗa 53 da 1447 ya zama 1,500 kenan daidai.
A bana Mauludin Manzon Allah SAW yana da wani girma na daban, na cewa Manzo SAW ya cika shekara 1500 kenan da haihuwa. Ya dace duk Musulmi, kai kowane ɗan Adam ma, tunda Manzo SAW ba namu ne mu kaɗai ba, da faɗin Ubangiji, “wama arsalnaka illa rahmatan lil’alamin – ba mu aikoka ba, face ka zama rahama ga duk halitta”, karatu ne mai girma mai tsawo mai faɗi. Ubangiji ya yi gaskiya.
Manzon Allah SAW abun kowa ya yi murna da shi ne, mun gode Allah, duk wanda yake da shekara 30 yaga yadda duniya ta yi murnar cikar Annabi Isah shekara 2000 da haihuwa, an yi bukukuwa, kuma ba wai Kiristoci kaɗai ne a lokacin suka yi bikin ba, domin Annabi Isah ba nasu ne su kaɗai ba. To ya dace duk Musulmi, mu yi ƙoƙari mu ke yin murnar na mu, zancen cewa yana da kyau ko bashi da kyau wannan daƙiƙanci ne, an wuce wannan lokacin. Babban littafin mu da muke dogaro da shi, Alƙur’ani, shi ne wanda Allah ya haɗo Manzo SAW da shi. Duk muhimmin abu idan ka saya (kamar rediyo, talabijin, wayar salula, da sauransu) sai kaga littafin da zai koya maka yadda ake amfani da wannan abun da ka siya (manual) a ciki, in kaƙi bin wannan littafi, ka bi son ranka, duk abin da ya faru babu ruwan kamfani. To muma ga littafin da Allah ya haɗo Annabinmu da shi, wanda duk ka’idojin addininmu suna ciki.
Allah ya yi mana Mauludin Annabawa wajen guda biyar a ciki. Allah SWT ya yi mana Mauludin farkon ɗan Adam ma, kuma ya ce mu yi yawo akan ƙasa don muga yadda ya fara halitta, wannan ita ce ayar da ta nuna mana mu yi ilimin binciken kasa sanin tsarinta (Archeology da Geology), don muga yadda Allah ya fara halittar ɗan Adam, da mazauninsa, da duk sana’arsa, da wayewarsa, ma’ana al’adunsa (culture), da cigabansa, da gine-ginensa. Sannan Allah ya yi mana maganar halittar Adamu, haka zalika kuma Allah yayi mana maganar farkon ciki da aka fara yi a doron ƙasa “HUWAL LAZI KHALAƊAKUM MIN NAFSIN WAAHIDA, WA JA’ALA MINHA ZAUJAHA LI YASKUNA ILAIHA. FALAMMA TAGASSHA HAMALAT HAMLAN KAFIFA…” , sannan Allah ya yi mana maganar haihuwar Annabi Musa da abubuwan da suka faru tsakaninsa da Fir’auna, ya yi mana maganar haihuwar Sayyida Maryam da sanya mata suna, ya yi mana maganar haihuwar Annabi Yahya, da Annabi Zakariyya, ya bamu labarin ya yi, shi Yahya ɗin nan Allah yayi masa ni’ima yace aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haifeshi da ranar da zai mutu, da ranar da za’a tasheshi ranar tashin ƙiyama.
Har ila yau, Allah yayi mana magana a faɗaɗe ta zancen haihuwar Annabi Isa (AS) da duk abinda ya faru. Annabi Isah shi ma ranar da aka haifeshi (ranar haihuwa fa ba wasa bace, rana ce mai haɗari domin ɗan zai iya mutuwa a ranar, Sannan kuma rana ce ta murna), Allah ya ce, “aminci ya tabbata a gare shi (Annabi Isa) ranar da aka haifeshi, da ranar mutuwarsa, da kuma ranar da za’a tashe shi (Ranar mutuwa ma rana ce mai girma, domin rana ce ta baƙin cikin an rabu da mamaci, amma shi kuma rana ce ta farin ciki a wajensa saboda rana ce da ya sadu da Allah).
Allah (SWT) ya faɗa mana Annabi Ibrahim (AS) ya roƙi Allah yazo da Annabi Muhammad (SAW), a lokacin da ya gina Makkah yayi roƙo Allah ya ba mutanen Makkah da duniya ma gaba ɗaya Annabi Muhammadu. Kuma Allah ya tabbatar da hakan a cikin Al’ƙurani mai girma. Sannan Allah yayi mana maganar haihuwar wanda ba Annabi ba ma, Sayyidina Ali Allah ya girmama fuskarsa ba Annabi bane, amma kuma Allah ya bamu labarin haihuwarsa a cikin Al’ƙurani “HUWAL LAZII KHALAFA MINAL MAA’I BASHARAN, FA JA’ALAHUU NASABAN WA SIHRA, WA KAANA RABBUKA FADIIRA” duk tafsirin duniya sunce maganar sayyiduna Ali ce. Sannan duk aron da muke yi ranar juma’a, da duk wannan Sallar juma’a da ake yi, saboda an halicci Adamu ne a cikinta.
Sannan kuma Allah yace yana faɗa ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama labarin Annabawa domin ya nutsar da zuciyarsa; ka dubi duk irin kyakkyawar zuciyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama amma ana bashi labarin Annabawa domin wannan zuciya tasa ta nutsu. Ka duba rukunnan hajji da muke yi idan munje, Safa da marwa, kifar sheɗan, da duk sauransu kai kace wasan kwaikwayo ne muke yi na yadda labarin Hajarah da Annabi Isma’il ya faru, amma kuma ibada ce muke yi, kaga kuwa tarihinsu ne. Ashe ba wasa bane kenan!
Ina kira ga al’ummar Musulmi mu guji yin maganganu wadanda basu da tushe, shi dai mauludi ana yine domin girmama Annabi Muhammad SAW, to tunda haka ne, akwai Shehi babba, wanda a ƙasara Makkah yake, Shehu Alawiy Malikiy, ya faɗa cewa “ace sai ranar Sha biyu ga Rabi’ul Awwal za’a yi Mauludi to in akwai bidi’a a ciki ma shi a wajensa wannan ne bidi’ar” akwai manyan waliyyai wadanda suma sun dauki duk ranar Litinin a matsayin ranar da suka keɓanta da azumi da yabon Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da niyyar Mauludi. Mu ma Alhamdu Lillahi duk ranar Litinin muna karanta suratun Najmi saboda abubuwan keɓanta na Manzon Allah da aka ambata a cikinta, mu ma muna karanta ta da niyyar Mauludi. Amma fa duk da haka ita ranar haihuwar tasa tana da wani keɓantaccen bambanci na musamman a kan sauran ranaku