’Yan Najeriya sun sha litar man fetur miliyan 63.7 a watan Disamba – NMDPRA

[ad_1]



Wani rahoton Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ya nuna cewa ’yan Najeriya sun sha man fetur har lita miliyan 63.7 a watan Disambar 2025.

Hukumar ta kuma ce daga cikin adadin, matatar mai ta Dangote ta samar da lita miliyan 32.02.

Rahoton ya ce kamfanin ya nuna ƙarfin amfani da damar samarwa a watan Disamba, inda ya kai kashi 71% daga cikin lita miliyan 50 da aka yi niyyar samarwa.

Ya ce samar da man fetur a watan Disamba 2025 ya ƙaru saboda samun karuwar daga masana’antar Dangote daga lita miliyan 19.5 a rana zuwa lita miliyan 32 a rana.

Hukumar ta bayyana cewa bayanan ba su haɗa da ajiyar man na masana’antar da aka ware don kasuwar cikin gida ba, domin bayanan da aka bayar sun ta’allaka ne da adadin da aka fitar zuwa kasuwar cikin gida ta manyan motoci.

Rahoton ya nuna cewa matatun mai uku na Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) ba su samar da ko da lita daya ba, domin a rufe suke ba sa aiki.

An ƙara da cewa saboda lokacin bukukuwa, NNPCL da sauran kamfanoni sun shigo da lita miliyan 42.2 a rana domin cike lita miliyan 72.4 na man da aka samar don kasuwar cikin gida.

Rahoton ya ƙara da cewa an bayar da lasisin sabuwar matatar mai ɗaya, yayin da Waltersmith (Train 2) mai karfin tace ganga 5,000 a kullum ta kammala shirye-shiryen fara aiki a watan Janairun 2026.

Dangane da matatun mai na zamani, rahoton ya ce Waltersmith ta yi amfani da kashi 63.24% na ƙarfin ta, ta samar da matsakaicin mai lita 51,000 a rana.

Matatar Edo ta yi amfani da kashi 85.43% na ƙarfin ta, ta samar da tsaka-tsakin man da ya kai lita 52,000 a rana, yayin da matatar Aradel wadda ta yi amfani da kashi 53.89% na ƙarfin ta ta samar da tsaka-tsakin mai lita 289,000 a rana.

Rahoton ya ce wadannan bayanai suna da muhimmanci domin suna nuna sauyin dabarun Najeriya a fannin makamashi, tare da rage shigo da mai daga waje, ƙarfafa samarwa a cikin gida, ƙirƙirar ayyukan yi, inganta tsaro, da tabbatar da daidaiton tattalin arziki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *