Ana zargin likitoci da manta almakashi a cikin matar da ta mutu a Kano

[ad_1]



Wani magidanci, Abubakar Muhammad, yana zargin Cibiyar Kula da Lafiyar Mafitsara ta Abubakar Imam da ke Jihar Kano da sakacin aiki wanda ya janyo mutuwar matarsa.

Magidancin dai yana zargin cewa mutuwar matarsa, Aishatu Umar, na da nasaba ne matsalar da ta biyo bayan wata tiyata da aka yi mata a asibitin.

Aminiya ta ruwaito cewa Aishatu Umar ta rasu ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a safiyar Litinin, inda ake zargin cewa an manta almakashin tiyata a cikin cikinta tun bayan aikin da aka yi mata.

Magidancin ya shaida wa Aminiya cewa matarsa wadda ta yi fama da rashin lafiya tsawon watanni da suka gabata, an yi mata tiyata a asibitin ne a watan Satumba.

Sai dai ya ce bayan an yi mata tiyatar ta riƙa fama da matsanancin ciwon ciki ba dare ba rana kuma abu ya ƙi ya ƙi cinyewa.

A cewarsa, duk lokacin da koma asibitin tana koke kan ciwon da take fama da shi, sai dai kawai a ba ta magungunan rage raɗaɗi ba tare da gudanar da cikakken bincike ba.

“Sau da dama suna faɗa mata cewa irin wannan ciwo ba kanta farau ba domin duk wanda aka yi wa tiyata yana fama da irin matsalar, amma ba su taɓa ba da shawarar a yi hoton X-ray ko wani bincike na musamman ba,” in ji shi.

Muhammad ya ce ciwon ya ci gaba har tsawon watanni huɗu, kafin daga bisani aka yi mata gwaje-gwaje da hotunan bincike a Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da kuma Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ’yan kwanaki kaɗan kafin rasuwarta.

Kamar yadda magidancin ya bayyana, sakamakon binciken, a cewar likitocin, ya nuna cewa an bar almakashin tiyata a cikin cikinta tun bayan aikin da aka yi mata a watan Satumba.

A cewarsa, har an fara shirye-shiryen sake yi mata wani aikin domin ciro almakashin, sai dai kafin hakan Aishatu Umar ta rasu.

Mijinta ya bayyana lamarin a matsayin babban sakaci, yana mai cewa ba wai kawai ya jefa iyalinsu cikin alhini ba, har ma jefa ayoyin tambaya masu nauyi game da ƙwarewa da kuma tsarin kula da lafiya.

“Mun san cewa mutuwa kaddara ce daga Allah, amma mun gaza fahimtar yadda irin wannan kuskure zai faru a aikin tiyata.

“Irin wannan lamari yana rage amincin jama’a a kan likitoci da cibiyoyin lafiya,” in ji shi.

Ya yi kira ga Gwamnatin Kano da hukumomin kula da aikin lafiya da su gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace, yana mai cewa dole ne a tabbatar da adalci.

Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, hukumomin asibitin ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin ba.

Mun fara bincike  — Hukumar Kula da Asibitocin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Babban Sakataren hukumar, Dokta Mansur Mudi Nagoda, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yana mai cewa binciken zai tantance gaskiyar abin da ya faru da har ya janyo matsalar.

“Mun miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan marigayiyar. Binciken zai kasance a bayyane, ba tare da son zuciya ba, kuma cikin ƙwarewa. Idan aka tabbatar da sakaci, za a ɗauki matakin da ya dace bisa ƙa’idoji,” in ji sanarwar.

Hukumar ta kuma tabbatar wa jama’a cewa lafiyar marasa lafiya ita ce ginshiƙinta na farko, tare da jaddada ƙudirin tabbatar da ingantaccen aikin kiwon lafiya a Jihar Kano.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *