Mun saki fursunonin siyasa 116 — Venezuela

[ad_1]



Gwamnatin Venezuela ta bayyana cewa kawo yanzu ta saki fursunonin siyasa 116 tun bayan sanarwar da ta yi a makon da ya gabata na fara sakin mutanen da aka tsare a zamanin tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, wanda sojojin Amurka suka cafke a wani samame da suka kai birnin Caracas.

Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da jam’iyyun adawa a ƙasar sun ce adadin mutanen da aka saki bai kai yadda gwamnati ta bayyana ba, inda a halin yanzu, iyalan waɗanda ke tsare ke ci gaba da taruwa a gaban gidajen yari, suna jiran tsammani kan makomar ’yan uwansu.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Gidajen Yari ta Venezuela ta ce sakin mutanen ya shafi “waɗanda aka tsare bisa zargin tayar da hargitsi, karya tsarin mulki da barazana ga zaman lafiyar ƙasa.”

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Foro Penal ta ce mutane 24 ne aka saki da safiyar Litinin, ciki har da ’yan ƙasar Italiya biyu.

Haka nan jam’iyyar adawa ta tabbatar da sakin wani jagoran matasa kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.

A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, Firaministan Italiya, Giorgia Meloni, ta gode wa gwamnatin rikon ƙwarya ta Venezuela ƙarƙashin jagorancin Delcy Rodriguez, tare da bayyana farin cikinta kan sakin ’yan ƙasar Italiya biyun.

Meloni ta ce ’yan ƙasar nata yanzu suna cikin tsaro a ofishin jakadancin Italiya da ke Caracas, kuma jirgi ya riga ya tashi daga Rome domin dawo da su gida.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun ƙiyasta cewa har yanzu akwai tsakanin fursunonin siyasa 800 zuwa 1,200 da ke tsare a Venezuela.

An sanar da shirin sakin fursunonin ne a ranar Alhamis da ta gabata, bayan matsin lamba daga Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya bayyana cewa Amurka ce ke da iko da al’amuran Venezuela, bayan kifar da Maduro tare da kai shi gidan yari a New York domin fuskantar tuhume-tuhumen safarar miyagun ƙwayoyi.

A ƙarshen mako ne Trump ya yi murnar sakin fursunonin, yana mai cewa yana fatan waɗanda aka saki za su “tuna irin sa’ar da suka samu bayan shigar Amurka domin yin abin da ya dace.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *