Yadda jami’in DSS ya sace ’yata ya sauya mata addini
Wani manomi mai shekaru 45 a Hadejia, Jihar Jigawa, Malam Abdulhadi Ibrahim, ya bayyana yadda iyalinsa suka shafe fiye shekara biyu suna neman ƙaramar ’yarsa Walida, wadda ake zargin wani jami’in Hukumar Tsaro ta DSS ya yi garkuwa da ita.
Malam Abdulhadi ya ce jami’in da ake zargi mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, ya tursasa wa ƙaramar yarinyar sauya addini daga Musulunci zuwa Kirista, sa’annan ya rika yi mata fyade har ta haihu a inda ya ɓoye ta.
Tuni dai wWata kotun majistare a Jigawa ta bayar da umarci Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar cafke jami’in na DSS, tare gudanar da “bincike mai zurfi kuma a asirce.” Kotun ta kuma umurci DSS da ta saki Walida nan take tare da haɗa ta da iyayenta.
Alkalin Kotun Majistare, Sadisu Musa ya bayar da umarnin ne bayan an shigar da karar hukumar Ifeanyi da sace Walida Abdulhadi, tursasa mata sauya addini, da kuma yi mata jerin cin zarafi na lalata har da ya kai ga samun ciki har ta haifi yaro.
Kotun ta ba da umarnin ne bisa roƙon da lauyan masu ƙara, Kabiru Adamu, ya gabatar na neman a tsare Onyewuenyi da kuma gudanar da bincike na hukuma kan zarge-zargen da ake yi ta hannun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, bisa tanadin Sashe na 125 da Sashe na 102(5) na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (ACJL).
Yadda Walida ta bace
Malam Abdulhadi ya shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi cewa Walida tana da shekara 16 kacal lokacin da ta ɓace daga gidansu.
“Ranar da ta ɓace, na ina gona. Da na dawo, na tambayi ina Walida, amma babu wanda ya san inda take. Mun neme ta ko’ina a Haɗejia, amma ba mu same ta ba,” in ji shi.
A cewarsa, tun farko ba a kai rahoton lamarin ga ’yan sanda ba, bisa shawarar dattawan danginsu. Ya ce lokacin, ya ba da shawarar kai ƙara, amma kakarta ta shawarce shi da a yi taka-tsantsan.
“Na roƙi kakarta ta bari mu kai rahoto wajen ’yan sanda, amma ta ce mu bari a yi addu’a. Ta ce ba za mu iya zargin kowa da sace ta ba, kuma ta shawarce ni da in ci gaba da addu’a, ina fatan Allah Zai bayyana inda take,” in ji Abdulhadi.
Ya ce bayan shekara biyu da watanni biyu na nema babu nasara, ga kuma da tsananin damuwa, sai wani abin mamaki ya faru.
“Wata rana bayan Sallar Isha’i, na samu kiran waya. Mutumin da ya kira bai iya Hausa sosai ba, sai wata mata da take jin Hausa sosai ta karɓi wayar, ta tambaye ni tsawon lokacin da ’yata ta ɓace. Da na ce shekara biyu da watanni biyu, sai ta ce, ‘Lallai kam, Walida ’yarka ce, tana tare da mu a Abuja,’” in ji shi.
Malam Abdulhadi ya ce masu kiran sun nemi ya zo Abuja, suna cewa za a aurar da ’yarsa ga ɗaya daga cikinsu.
“Na firgita ƙwarai. Na tambaya ta yaya hakan zai faru? Wannan hauka ne,” in ji shi, yana cewa ya sanar da su cewa yana Haɗejia, amma ya ba su lambar wayar ɗan uwansa da ke zaune a Abuja.
Inda aka ɓoye ta
Ɗan uwan Walida, Muhammad Badamasi Ibrahim, wanda ke zaune a unguwar Karmajiji, kan hanyar Filin Jirgin Sama a Abuja, ya tabbatar da labarin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin girgiza.
“Ranar 1 ga Janairu, da misalin ƙarfe 10 na safe, ƙannena suka kira ni suka ce an gano Walida a Abuja. Na shiga firgici matuƙa. Tsawon fiye da shekara biyu babu wanda ya ji wani labari a kanta,” in ji shi.
Muhammad ya ce daga bisani ya tuntuɓi masu kiran, inda aka umarce shi ya je wani wuri a kusa da Kuchigoro, kan hanyar Filin Jirgin Sama, sannan daga nan aka ce ya je wani wuri da ya bayyana a matsayin gidajen DSS.
“Da na isa can, sai aka ce in nemi wani mai suna Victor. Na tarar da wani mutum zaune a kujera, ya ce yarinyar tana tare da wani abokin aikinsu kuma za a aura masa ita,” in ji shi.
Muhammad ya ce, ya ƙi amincewa da hakan, saboda dalilai na addini.
“Addininmu, Musulunci, bai yarda Kirista ya auri Musulma ba. Yarinya ta ɓace tana ƙarama, yanzu kuma suna maganar aure,” in ji shi.
A cewar Muhammad, duk ƙoƙarin da suka yi na ganin an saki Walida ya ci tura.
“Sun ce ba za su sake ta ba. Har ma suka ce idan ta koma gida za su kashe ta. Na ji tsoro sosai a yayin tattaunawar,” in ji shi, yana mai cewa an faɗa masa ko da an kai lamarin kotu, za a warware shi ta hanyar sulhu.
“An yi wa ’yata ciki, an sauya mata addini”
Abdulhadi ya ƙara da cewa an sauya wa ’yarsa addini zuwa Kiristanci, an yi mata ciki, sannan aka yi mata tiyatar haihuwa (CS) domin ba ta kai girman da za ta haihu da kanta ba.
“Yaren da take magana ya sauya gaba ɗaya. Na gane muryarta ne kawai saboda ni ne mahaifinta. An yi mata ciki, ta kuma haihu ta hanyar CS. Wata mata mai suna Gloria, wadda aka ce likita ce kuma ’yar uwar mutumin ce, ita ce ta kula da haihuwar,” in ji shi.
Ya ce wannan doguwar azaba ta yi mummunan tasiri ga iyalinsa, inda ya bayyana cewa mahaifiyar Walida ta rasu watanni biyu da suka wuce, bisa zargin baƙin ciki da damuwar ɓacewar ’yarta.
“Mahaifiyarta ta mutu tana cikin ciwon damuwar rashin sanin inda ’yarta take. Wannan wahala ta tarwatsa iyalinmu,” in ji shi.
Malam Abdulhadi ya ce yanzu lauyoyi daga Jihar Jigawa ne ke kula da lamarin, kuma an ɗauki matakai na kai rahoto ga hukumomin da suka dace.
“Mun je ofisoshin DSS a Abuja sau da dama. Mun kuma kai lamarin kotu, mun bayyanar da shi ga jama’a domin a samu adalci,” in ji Abdulhadi.
DSS ta tsare jami’inta
A halin da ake ciki, Hukumar Tsaro ta DSS ta tsare jami’in nata da ake zargi da sace karamar yarinya a Jihar Jigawa.
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Sadarwa na DSS, Favour Dozie, ya ce hukumar ta tsare wanda ake zargi bisa umarnin kotu.
“An ja hankalin DSS zuwa rahotannin da ke zargin wani ma’aikacinmu, Ifeanyi Festus, da hannu a sacewa, lalata da ƙaramar yarinya da kuma cin zarafin matsayinsa, da sauransu.
“Don fayyacewa, hukumar ba ta da wani ma’aikaci da ke ɗauke da sunan da aka ambata.
“Amma muna tabbatar da cewa wani ma’aikacinmu mai aiki, Ifeanyi Onyewuenyi, wanda ake zargi da tilasta wa Walida Abdulhadi sauya addini da kuma aurenta, an cafke shi kuma ana binciken sa.
“Muna jaddada cewa irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa ƙa’idojinmu da kundin ɗabi’a. Za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a,” in ji DSS a wata sanarwa.
Lamarin ya biyo bayan wani ƙorafi da ƙungiyar lauyoyi ta Gamji Lawchain ta shigar, a madadin mahaifin Walida.
Korafin ya zargi jami’in da sace Walida fiye da shekara biyu da suka wuce, tsare ta ba bisa ƙa’ida ba, cin zarafinta ta fuskar lalata, da tilasta mata sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da amincewar iyaye ba. Haka kuma ya ce ta haihu tana ƙarama.
Korafin ya yi Allah wadai da cin zarafin iko, yana neman dakatarwa, tsarewa da gurfanar da wanda ake zargi, tare da bincike mai zaman kansa kan ofishin DSS.
Sun kuma buƙaci a tabbatar da kare lafiyar wadda abin ya shafa, a haɗa ta da iyalinta, tare da ɗaukar mataki kan duk wani ma’aikacin DSS da aka samu da hannu.
Ƙungiyar lauyoyi ta nemi adalci ga iyalin Walida
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Dutse a Jihar Jigawa, ta buƙaci a gaggauta gurfanar da jami’in DSS, Ifeanyi Onyewuenyi, da ake zargi da sace ƙaramar yarinya, ya yi mata fyaɗe tsawon shekara biyu da tilasta mata sauya addini.
A wata sanarwa da Shugaban reshen, Barr. G. H. Umaru, ya fitar ranar Asabar, ya ce DSS ta bi umarnin Babbar Kotun Majistare ta Haɗejia da aka bayar ranar 7 ga Janairu, 2026, na cafke wanda ake zargi nan take, bincikensa, tare da sakin yarinyar ga iyalinta.
NBA ta amince da rahoton cafke wanda ake zargi da DSS ta yi, tare da buƙatar “cikakken bin umarnin kotu nan take daga dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa.”
Haka kuma ta buƙaci “bincike mai sauri, bayyananne, zurfi kuma ba tare da son zuciya ba, domin tantance laifin wanda ake zargi da duk wasu masu hannu a wannan mummunan lamari.”
Reshen NBA na Dutse ya ce zai ci gaba da sa ido kan lamarin tare da tabbatar da cewa “baya ga yin adalci, a ga an yi adalci ga Malama Walida Abdullahi da iyalinta.”
Ta kuma yi kira ga dukkan ɓangarori da jama’a su zauna lafiya tare da bin doka yayin da bincike da shari’a ke tafiya.