Sin Da Tanzania Sun Yi Alkawarin Karfafa Hadin Gwiwa

[ad_1]

Bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Tanzania Mahmoud Thabit Kombo ya yi masa, memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kai ziyara kasar Tanzania, tsakanin ranekun 9 da 10 ga watan da muke ciki.

Yayin zantawar da ministocin biyu suka yi, sun darajanta dadadden zumuncin dake wanzuwa tsakanin kasashen 2, bisa tushen imani da girmama juna. Kana sun nuna gamsuwa ga dimbin sakamakon da aka cimma, bisa hadin gwiwar da kasashen Sin da Tanzania suke yi, cikin shekaru fiye da 60 da suka gabata.

Ban da haka, yayin ganawar ministocin kasashen 2, an tabbatar da niyyar dunkule tsare-tsaren raya kasa na bangarorin 2 waje daya, da habaka hadin gwiwarsu ta fuskar al’adu, da yawon shakatawa, da ilimi, da kula da lafiyar jama’a, da wasannin motsa jiki, da harkoki masu alaka da hakkin samari da ‘yan mata, da cibiyoyin masana, da kafofin watsa labaru, da dai sauransu.

Haka zalika, a madadin gwamnatocin kasashensu, ministocin harkokin waje na kasashen Sin da Tanzania, sun jaddada bukatar kare kundin dokar Majalisar Dinkin Duniya, da girmama ikon mulkin kai, da hurumin yankunan kasa na kasashe daban daban, sun kuma yi kira da a ko da yaushe, a tsaya kan manufar daidaita bambance-bambance ta hanyar tattaunawa. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *