Ruwan sama da guguwa sun lalata gidaje da Sakatariya a Jos
[ad_1]
Ruwan sama da iskar guguwa da aka yi kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba sun yi sanadin lalata gidaje da dama a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Ruwan sama ya kuma lalata sassan sakatariyar Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
Ruwan da aka yi kamar da bakin ƙwarya ya yi ɓarna a yankin Bukur da ke Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar, Silas Patrick Dung ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba a Jos, inda ya bayyana cewa guguwar ta yi ƙarfi matuƙa, inda ta tumbuke ginshiƙai huɗu da ke riƙe da babbar ƙofar Sakatariyar tare da lalata wasu gidaje a cikin unguwanni.
Ya ce, “Kamar yadda guguwar ta lalata ƙofar Sakatariyar Majalisar, wadda aka gina da ƙarafuna masu ma’aunin 25mm, ya nuna cewa guguwar ta yi ƙarfi sosai.”
Shugaban Ƙaramar Hukumar wanda ya ziyarci wuraren da lamarin ya shafa tare da jami’an Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ya bayyana cewa guguwar ta lalata wasu gidaje, yayin da wasu da dama kuma rufin su ya lalace tare da lalata katangar gidaje.
Dung ya danganta ɓarnar da iska mai ƙarfi ta yi, yana mai bayyana ta a matsayin iftila’i.
Ya ce hukumomi na bakin ƙoƙarinsu domin tantance yawan ɓarnar da aka yi tare da bayar da tallafi ga mutanen da abin ya shafa, tare da bayar da tabbacin cewa majalisar za ta ɗauki matakan da suka dace don hana afkuwar lamarin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link