Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

[ad_1]

A duk yayin da mace ta dauki ciki, tana samun kanta a wani irin yanayi maras dadi har sai ta haihu, don haka; batun juna biyu ba karamin al’amari ba ne, sakamakon zuwa da ya ke yi da hadari iri daban-daban.

Wasu matan, bayan sun dauki ciki ne suke haduwa da cututtuka da dama; kamar ciwon zuciya, ciwon siga, hawan jini da sauran makamantansu. Don haka, a nan ya kamata a sani cewa; babu yadda za a yi mace ta dauki ciki ba tare da jikinta ya canza ba.

  • Shettima Ya Ce Zuba Jari A Ɓangaren  Ilimi Ba Caca Ba Ce
  • Wang Yi Ya Yi Tsokaci Dangane Da Dalilan Dadaddiyar Al’adar Ziyarar Da Ministocin Harkokin Wajen Sin Ke Fara Yi A Afirka A Duk Shekara

Wannan dalili ne ya sa, idan nauyin mai juna biyu bai kai yadda ake bukata ba, sai a ja hankalinta ta yi wasu abubuwa da za su sa nauyin nata ya karu, haka nan; idan nauyin nata ya yi yawa, musamman ga mata masu kiba; nan ma a kan ja hankalinsu su yi kokari wajen rage nauyin nasu.

Saboda haka, da zarar an ce mace na da ciki; abubuwa da dama na sauya yanayin jikinta, wata ta kara kiba, wata kuraje su feso mata a fuska, wata kalar fatarta ta canja; wani wajen ya yi fari wani ya yi baki, wasu su yi ta samun kananan cututtuka, wasu amai, wasu kuma saboda damuwa su yi ta faman kuka ba tare da an yi musu komai ba.

Don haka, ya zama wajibi maza su rika yi wa matansu uzuri a yayin da suke dauke da juna biyu da kuma bayan sun haihu. Misali, babu yadda za a yi a ce mace ta dauki ciki tsawon wata tara tana tare da shi, sannan bayan ta haihu a kuma yi tunanin cewa; wannan ciki nata zai dawo kamar yadda yake a baya.

Har ila yau, maza da dama na da irin wannan dabi’a ta tsangwamar matansu, sakamakon yadda jikinsu yake sauyawa bayan sun haihu, musamman ganin yadda cikinsu yake yin shaida ko tattarewa ko kuma girma ta hanyar samun tumbi.

Irin wannan tsangwamar da maza ke yi wa mata, ko kadan bai dace ba; domin kuwa wasu matan na shiga cikin mummunan hali tare da takurawa kansu, ta hanyar kashe kudadensu don ganin sun samu maganin wannan matsala, wadda babu yadda za a yi a iya magance ta, tunda halittar ce a haka; kamar shekaru ne duk yadda za ka yi, babu wata dabara da za ta iya boye su.

Saboda haka, mata ya kamata ku kiyaye; ku daina zuwa kuna kashe kudadenku babu gaira babu dalili, amma babu wani magani da za a baki ki sha tumbinki ya tafi, wasu sai su sha magani su je su yi ta zawo haka kawai, wai don tunbinsu ya ragu.

A nan, muna kara jan hankalin maza; su ji tsoron Allah su rika tausaya wa matayensu, musamman bayan sun samu juna biyu sun haihu. Sannan ku tuna cewa, wannan ciki da yake canja wa mata wasu bangarori na jikinsu, ku ne kuke yi musu ba daga gidajensu suke zuwa da shi ba.

Daga rumbun Dakta Na’ima Abubakar

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *