Gwamnatin Tarayya Da ASUU Za Su Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya Ranar 14 Ga Janairu
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) na shirin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a ranar Laraba, 14 ga Janairu, domin ƙarfafa zaman lafiyar aiki da inganta yanayin koyo da karatu a jami’o’in Nijeriya. Wannan na ƙunshe ne cikin wata gayyata a hukumance da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta gayyaci shugabannin jami’o’in tarayya domin halartar bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a Abuja.
Bikin, wanda aka shirya gudanarwa da ƙarfe 11:00 na safe, zai ƙunshi muhimman tanade-tanade da suka haɗa da ƙarin albashi kashi 40 cikin 100 ga malaman jami’a, da kuma inganta tsarin fansho. Daga cikin sabbin sharuɗɗan, farfesoshi za su yi ritaya ne suna da shekaru 70, tare da karɓar fansho da ya kai daidai albashinsu na shekara gaba ɗaya, wata muhimmiyar buƙata da ASUU ta daɗe tana nema.
- AFCON 2025: Hukumar CAF Ta Sauya Alƙalin Da Zai Jagoranci Wasan Nijeriya Da Algeria
- ASUU Ta Yi Watsi Da Ƙarin Albashin Kashi 35, Ta Buƙaci A Bai Wa Jami’o’i Isassun Kuɗi
Sabuwar yarjejeniyar ta kuma tanadi sabon tsarin tallafin kuɗaɗe ga jami’o’i, inda za a ware kuɗi na musamman domin bincike, da ɗakunan karatu, da ɗakunan gwaje-gwaje, da kayan aiki da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata.
Ma’aikatar Ilimin ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban ci gaba a tattaunawar da aka daɗe ana yi tsakanin gwamnati da ASUU, tare da nuni da cewa hakan na nuna ƙudirin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a fannin ilimi.
An cimma matsayar yarjejeniyar ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, bayan kammala sake tattauna yarjejeniyar 2009 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, lamarin da ya kawo ƙarshen rikicin aiki da ya shafe sama da shekaru 16.
Yarjejeniyar za ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, tare da duba ta bayan shekaru uku, kuma ta haɗa da shirin kafa Hukumar Bincike ta Ƙasa wadda za ta tallafa wa bincike da aƙalla kashi ɗaya cikin ɗari na GDP na Nijeriya, daidai da Manufar “Sabunta Fata” ta Shugaban Ƙasa.
[ad_2]
Source link