Za a sami raguwar hauhawar farashin kaya sosai a 2026 – Tinubu

[ad_1]



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen cewa za a samu ƙarancin hauhawar farashin kaya sosai a shekarar 2026 inda ya ce hauhawar za ta iya sauka zuwa ƙasa da kashi 10 cikin 100.

“Lallai, hauhawar farashin kaya na iya sauka zuwa ƙasa da kashi 10 cikin ɗari kafin ƙarshen wannan shekara, wanda zai haifar da ingantacciyar rayuwa da hanzarta girman tattalin arziki. Shekarar 2026 za ta kasance shekara ta tarihi wajen kawo wadata ga duk ’yan Najeriya,” in ji Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaban Kasar.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa inda ya yaba wa kamfanonin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar hannayen jari ta Najeriya saboda jarinta ya zarce Naira tiriliyan 100 a darajar kasuwa.

Ya yi alkawarin cewa tare da ci gaba da gyare-gyaren tattalin arziki da ake yi, wanda ake sa ran zai kawo riba mai yawa, shekarar 2026 za ta kasance mafi alheri ga masu zuba jari a ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa kasuwar hannun jarin ta cimma burin darajar kasuwa ta Naira tiriliyan 100 a ranar Litinin, inda bayanai suka nuna darajar kasuwar ta rufe a Naira tiriliyan 101.80.

Darajar kasuwa na nuna jimillar darajar hannayen jarin kamfanoni da ke kasuwar hannayen jari.

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana wannan nasara a matsayin abar ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari da ke aiki a kasuwar kuɗi da hannayen jari.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zurfafa zuba jari a cikin tattalin arzikin cikin gida, yana tabbatar da cewa “shekarar 2026 za ta samar da ribar da ta fi girma yayin da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatinsa ke ci gaba da kawo sakamako mai ƙarfi.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *