INEC Ta Fara Kashi Na Biyu Na Rajistar Masu Zabe
[ad_1]
Hukumar zabe mai zman kanta (INEC) ta ci gaba rajista masu son a basu katin zabe a fadin tarayyar Nijeriya, shi ne kuma kashi na biyu da aka fara.
Shirin da aka fara ne ranar Litinin ta wannan makon,ya biyo bayan wanda aka kammala ranar 10 ga Disamba, 2025 wanda kuma shi ne na farko.
- Ma’aikatar Tsaro Na Amfani Da Ofishin NSA Wajen Gallaza Wa ’Yan Adawa – Gwamnatin Zamfara
- APC Ga Atiku: Dimokuraɗiyyar Nijeriya Ba Ta Cikin Barazana
Tun farko hukumar ta fara shirin raijstar ne ta kafar sadarwa ta zamani ranar 18 Agusta, 2025, kafin a fara da mutum zai je da kan shi ya yi, a cibiyoyin da aka zaba ranar 25 ga Agusta, 2025.
A bayanin da aka yi cikin watan Disamba, hukumar ta bayyana ‘yan Nijeriya milyan 9,891,801 ne suka yi rajista lokacin da aka fara shirin ta kafar sadarwa ta zamani.
Daga cikin su, mutane milyan 2,572,054 aka kammala yi masu rajistar zuwa 28 ga Nuwamba 28, 2025, wannan ya hada da 1,503,832 wadanda suka yi ta kafar sdarwa ta zamanion da kuma 1,068,222 da suka je da kansu suka yi rajistar.
Hukumar tace an yi amfani da tsaikon da aka samu tsakanin nau’iin rajistar biyu wajen yin wasu abubuwan da doka ta bukata ayi, da suka hada da yadda aka baje sunayen ne saboda idan an samu wasu masu korafi na idan anyi wani kuskure sai a gyara.
“Kmar yadda sashe na 19 na dokar zabe ta 2022, baje sunayen wadanda suka yi rajista domin idan akwai masu korafi kan abinda yake cikin rajista an yi hakan tsakanin 15 zuwa 21 ga Disamba,2025,a ofisoshin kananan hukumomi,”kamar yadda hukumar ta ce.
Sai dai kuma hukumar tace tsarin CBR ba ayi shi ba a Jihar Anambra da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) saboda ayyukan zaben da ake yi a wuraren.Za ‘a sanar da eanakun da za’a yi abubuwan a Anambra da kuma FCT nan gaba.
[ad_2]
Source link