Ko Me Matakin Amurka Na Tusa Keyar Shugaban Venezuela Ka Iya Haifarwa?
[ad_1]
Idan ba mu manta ba a farkon makon nan ne shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya gurfana gaban wata babbar kotun gundumar Manhattan ta birnin New York, bayan da gwamnatin Amurka ta yi amfani da karfin soji wajen tusa keyarsa daga kasarsa zuwa Amurka, a wani yanayi da masharhanta ke ganin na nuni ga yadda Washington ke keta hurumin dokokin kasa da kasa da ikon mulkin kai na sauran kasashe.
Duniya ta ga baiken wannan mummunan mataki da Amurka ta aiwatar, bayan Allah-wadai daga sassa daban daban, masu fashin baki na ganin yin garkuwa da shugaban wata kasa mai cin gashin kai, da gurfanar da shi a kotun wata kasa ta daban ba shi da wata alaka da aiwatar da doka. Maimakon hakan mataki ne dake tabbatar da akidar gwamnatin Amurka mai ci a halin yanzu na kasancewa ’yar kama-karya.
To ko me wannan mataki na Amurka ka iya haifarwa ga tsarin diflomasiyyar duniya? Da yawa daga masu nazarin wannan al’amari na ganin matakin na Amurka, ya nuna wani mummunan misali ne ga sauran sassa masu ra’ayin murdiya, cewa duk wata kasa mai karfi na iya aiwatar da matakin kashin-kai ga wata kasa ta daban, wanda hakan tabbas zai kai ga haifar da salon “kashin-dankali”, wato har kullum manya su danne kanana.
Kowa ya san cewa, bisa odar kasa da kasa, ba wani bangare da ke da halastaccen iko na zama dan sandan duniya shi kadai, kana ba wata kasa dake da ikon mayar da kanta alkaliya kan sauran kasashe. Duk wani mataki da za a iya dauka don warware takaddama tsakanin sassan kasa da kasa, alhaki ne da ya rataya a wuyan hukumomin kasa da kasa a jimlace.
Akwai ma masu ganin matakin kame shugaban Venezuela, tsantsar kwadayi ne na albarkatun man kasar. Shaida kan hakan kuwa ita ce yadda jim kadan da kama shugaban kasar, shugaban Amurka ya yi kira ga wadda aka nada mukamin rikon kwaryar shugabancin Venezuela Delcy Rodriguez, da ta baiwa Amurka damar yin cikakken iko da albarkatun man kasar.
Ko shakka babu, duniya ba ta bukatar ’yan katsa-landan, ko masu keta hurumin dokokin kasa da kasa. Abun da duniya ke bukata shi ne gina al’umma mai makomar bai daya, wadda dukkanin bangarorinta za su rika cudanya bisa mutunta ikon mulkin kai, da martaba dokokin kasa da kasa, da sauke nauyin dake bisa wuyansu ta hanyar tabbatar da tasirin mabanbantan sassan kasa da kasa.
Ya zama wajibi a kare hakkoki, da tsaron yankunan dukkanin kasashen duniya kanana da manya, bisa tanadin dokokin kasa da kasa, ba wai rungumar tsarin kama-karya da babakere ba! (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link