Sama da mutane 20 sun ɓace
[ad_1]
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyana cewa, ya zuwa rana r Laraba an ceto mutane 25 daga cikin fasinjoji sama da 50 da ke cikin kwale-kwalen da ya yi hatsari a Jihar Sakkwato.
Hukumar NEMA ta ƙara da cewa kawo yanzu an gano gawarwaki uku a hatsarin kwale-kwalen.
Ya ce, kawo yanzu an ceto mutane 25 daga cikin fasinjoji sama da 50 da ke cikin jirgin.
Sai dai hukumar NEMA ta ce ta kammala aikin bincike da ceto.
Shugaban ofishin Hukumar NEMA na Sakkwato, Aliyu Kafindangi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
“Kwanaki uku da suka gabata, muna cikin aikin ceto bayan da wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ’yan kasuwa da mata ya kife.
“Kwale-kwalen ya kife ne a ranar Lahadin da ta gabata tare da fasinjoji sama da 50. Sa’ar da aka yi, an ceto mutane 25 da ransu. Sannan washegari, an ci gaba da neman ceton wasu, amma ba mu samu nasarar ƙara buɓutar da kowa ba,” in ji Kafindangi a cikin tattaunawarsa da tashar Talabijin ta Channels The Morning Brief.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link