ICPC Za Ta Ci Gaba Da Binciken Tsohon Shugaban NMDPRA Duk Da Janye Ƙarar Dangote
[ad_1]
ICPC ta ce za ta ci gaba da binciken tsohon Shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, duk da cewa attajirin ɗan kasuwar nan, Aliko Dangote ya janye ƙorafinsa.
Hukumar ta tabbatar da cewa Dangote ya aike mata wasiƙar na janye ƙorafinsa.
- Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi
- Za Mu Baza Ƙarin Jami’anmu A Faɗin Nijeriya Don Samar Da Tsaro – Sojoji
Duk da haka, ICPC ta jaddada cewa tana da ikon ci gaba da binciken Tsoho shugaban hukumar.
Ƙorafin ya biyo bayan saɓanin da aka samu tsakanin Dangote da Ahmed a shekarar 2025.
Dangote ya zargi Ahmed da cin hanci, inda ya ce ya kashe miliyoyin daloli wajen ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yansa a ƙasashen waje, kuɗin da bai dace da albashin jami’in gwamnati ba.
Daga baya Ahmed ya yi murabus daga muƙaminsa.
ICPC ta ce bincike na gudana don tabbatar da gaskiya da adalci, da kare muradun jama’a.
Jami’an hukumar sun kuma jaddada cewa binciken zai duba dukkanin ɓangarori, ciki har da yadda aka yi amfani da kuɗaɗen gwamnati, duk da janye ƙorafin Dangote.
[ad_2]
Source link