Matasa 2 sun shiga hannu kan yunƙurin yi wa fursunoni safarar wiwi a kotu

[ad_1]



Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), a Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa yunƙurin kai wa fursunoni miyagun ƙwayoyi a harabar Kotun Majistaren Nomansland.

Matasan da aka kama su ne Usman Khalid mai shekara 25 da Bello Musa Ahmed mai shekara 24.

Dukkaninsu mazauna Tsamiya ne da ke unguwar Brigade a Jihar Kano.

Jami’an tsaron Gidan Gyaran Hali na Goron Dutse ne suka kama su yayin da suke ƙoƙarin jefa wa fursunoni tabar wiwi a cikin harabar kotun.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya gargaɗi jama’a da su guji yin alaƙa da fursunoni, musamman a lokacin da aka kai su kotu ko dawowa da su daga kotu.

Ya ce irin wannan aiki barazana ce ga tsaro kuma doka ta haramta shi, kuma an tanadar masa hukunci mai tsanani.

Ya ƙara da cewa Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta jajirce wajen gyarawa da tarbiyyar fursunoni, kuma ba za ta lamunci duk wani yunƙuri da zai kawo cikas ga wannan aiki ba.

Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Gyaran Hali na Jihar Kano, Ado Inuwa, ya bayar da umarnin a miƙa mutanen da aka kama tare da ƙwayoyin da aka ƙwato ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) domin ci gaba da bincike da kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Hukumar ta sake jaddada cewa ba ta yadda da amfani da duk wasu miyagun ƙwayoyi a gidajen gyaran hali ko harabar kotuna ba.

Ta roƙi jama’a da suke bai wa hukumomin tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da doka a ƙasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *