Amurka Za Ta Rasa Matsayinta Na Jagorancin Duniya – Mahdi Shehu

[ad_1]

Masani kan harkokin siyasa, Mahdi Shehu, ya ce wata rana Amurka za ta rasa matsayinta na ƙasar da ke jagorantar duniya.

Ya zargi Amurka da tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe, yana cewa tana yin kamar ita ce ‘yansandan duniya maimakon mayar da hankali kan matsalolinta na cikin gida, musamman matsalar rashin tsaro.

  • Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
  • Sojoji Sun Tarwatsa Gungun Masu Tayar Da Bam A Adamawa

Shehu ya ce barazanar Amurka a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini, sai dai albarkatun ƙasa da Allah Ya albarkaci ƙasar da su, musamman ma ma’adinai masu daraja.

Ya kuma zargi ƙasashen Yamma da hana Nijeriya samun fasaha da horon da take buƙata domin yaƙi da matsalar tsaro.

Ya ƙara da cewa ya dace Nijeriya ta ƙarfafa dangantaka da ƙasashe kamar China da Rasha, waɗanda a cewarsa muradunsu sun fi na Amurka kyau.

A cewarsa, ayyukan gine-gine da China ke tallafawa sun fi bayyana, yayin da rancen kuɗi da ake karɓowa daga ƙasashen Yamma na jefa ƙasashe masu tasowa cikin matsin tattalin arziƙi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *