Mutum 7 sun mutu a artabu tsakanin sojojin Syria da dakarun Kurdawa

[ad_1]



Aƙalla mutane bakwai, mafi yawansu fararen hula, sun rasa rayukansu sakamakon artabu tsakanin sojojin gwamnati da dakarun Kurdawa a birnin Aleppo da ke Arewacin Syria.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, ɓangarorin biyu na zargin juna da assasa wutar rikicin, wanda ya samo asali daga tangarɗar aiwatar da yarjejeniyar haɗa dakarun Kurdawa da sabuwar gwamnatin Syria, wadda har yanzu ba a iya cimma ta ba.

Rikicin ya fi shafar unguwannin Sheikh Maqsud da Ashrafiyeh, masu rinjayen Kurdawa, inda aka yi amfani da manyan makamai, ciki har da harsasai da makamai masu linzami.

Turkiyya ta buƙaci dukkan ƙungiyoyin Kurdawa masu ɗauke da makamai, ciki har da na Syria, su miƙa makamansu, tana mai cewa ba za ta amince da kafa sansanin ‘yan ta’adda a kusa da iyakarta ba.

Rikicin na daga cikin mafi muni tun bayan kifar da tsohon shugaban ƙasar Syria, Bashar al-Assad, kuma ya ƙara nuna irin ƙalubalen da ke tattare da shirin haɗa dakarun Kurdawa cikin rundunar gwamnati.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *