Jam’iyyar ADC ta kori mutumin da ya yi ikirarin zama shugabanta na kasa

[ad_1]



Jam’iyyar kawancen ’yan adawa ta ADC a jihar Gombe sanar da korar mutumin nan da ya yi ikirarin zama sabon shugabanta na kasa, Nafiu Bala, daga jam’iyyar gaba daya.

Kazalika, jam’iyyar ta kuma ladabtar da wasu manyan jiga-jiganta su uku, bayan zargin aikata ayyukan da suka saba wa manufar jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Malam Auwal Abba Barde ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Gombe ranar Alhamis.

Ya ce an kori Nafiu Bala daga jam’iyyar ne bayan ya ayyana kansa a matsayin shugabanta na ƙasa tare da sauke wasu mutum uku daga mukamansu.

Wadanda aka sauke din a cewar shugaban sun haɗa da Mataimakin Shugaban jam’iyyar na Jiha, Nasiru Lawan da Sakatarenta, Danladi Ya’u da kuma Shugaban Matasa, Abdulkadir Sa’idu Digiri.

Barde ya ce sun gayyaci Nafi’u ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na Nasarawo domin kare kansa amma ya ƙi amsa kiran, wanda hakan ne ya sa aka same shi da laifin rashin da’a ga jam’iyyar.

Ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta lamunci cin amanar jam’iyya ko rashin biyayya ba, tare da tabbatar da cewa ADC ta ci gaba da samun haɗin kai yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

A farkon watan Yuli ne dai gamayyar hadakar ’yan adawa a Najeriya suk rungumi jam’iyyar ADC sannan suka ayyana tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, David Mark a matsayin shugaban riko na kasa.

Kazalika, jam’iyyar ta zabi tsohon Gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatarenta na kasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *