Da Ɗumi-ɗumi: Manchester United Ta Sanar Da Korar Kocinta Ruben Amorim

[ad_1]

Daga Rabilu Sanusi Bena

Manchester United, a ranar Litinin, ta tabbatar da cewa Babban Kocin kungiyar, Ruben Amorim ya bar matsayinsa nan take, Amorim, wanda aka nada a watan Nuwamban shekarar 2024, ya jagoranci kungiyar zuwa wasan karshe na UEFA Europa League a Bilbao a watan Mayun da ya gabata.

Duk da kaiwa wasan karshe a gasar ta Turai, shugabannin kungiyar sun yanke shawara mai wahala ta rabuwa da kocin dan kasar Portugal, a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna cewa, duk da kasancewar Manchester United a halin yanzu tana matsayi na shida a gasar Premier League, kungiyar na bukatar ta canza alkibla domin ganin ta samu abinda take nema a wannan kakar.

Kungiyar ta nuna godiyarta ga Amorim saboda gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake aiki, sannan ta yi masa fatan alheri aikinsa na gaba, kocin karamar kungiyar Manchester United Darren Fletcher zai jagoranci kungiyar na wucin gadi a wasan da za su yi da Burnley a gasar Premier League ranar Laraba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *